Babu kasar da tafi Najeriya yawan yara maras zuwa makaranta, Bankin Duniya

Babu kasar da tafi Najeriya yawan yara maras zuwa makaranta, Bankin Duniya

  • Najeriya ce ta daya a duniya cikin jerin kasashe mafi yawan yara marasa zuwa makarantu a duniya
  • Bankin duniya a rahotonsa ya bayyana cewa yara yan shekaru 6 zuwa 15 sama da milyan 11 basu zuwa makaranta
  • Bincike ya nuna cewa adadin yara maras zuwa makaranta a Najeriya ya tashi daga milyan 10 zuwa 18, gidauniyar MacAuthur

Bankin Duniya ya bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya.

Bankin yace kawo shekarar 2020, yara milyan 11 ne ba su zuwa makaranta gaba daya, rahoton Vanguard.

Wannan ya bayyana ne a rahoton da bankin ya saki ba take "Bayanai kan abubuwan dake gudana a Najeriya (June 2020).

A cewar rahoton,

"Duk da cewa Najeriya ta inganta hanyoyi samun ilimi a shekaru baya-bayan nan. har yace itace ta daya wajen adadin yara marasa zuwa makaranta a duniya."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Yi Wa INEC Katsalandan Ba, In Ji Buhari

"Najeriya na da sama da yara milyan 11 maras zuwa makaranta kuma yan shekaru 6 zuwa 15."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

yaran
Babu kasar da tafi Najeriya yawan yara maras zuwa makaranta, Bankin Duniya Hoto: Yara

Adadin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya kai milyan 18, Gidauniyar McArthur

Gidauniyar MacArthur ta bayyana cewa duk da kudi N100trn da gwamnatin Najeriya tayi ikirarin kashewa kan Ilimi daga 1999 zuwa yanzu, adadin yaran da basu zuwa makaranta ya kusa milyan ashirin.

Gidauniyar tace adadin yara ya tashi daga 10.5 milyan zuwa 18 milyan.

Mataimakin Diraktan gidauniyar dake Najeriya, Dayo Olajide, ya bayyana haka a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja wajen taron tattaunawa kan ayyukan mazabu da yakin neman zaben 2023.

Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF

Kwanakin baya, asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce kashi 70 cikin 100 na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai da ake koya musu a makaranta.

Kara karanta wannan

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

Masanin sadarwa na UNICEF, Mr Geoffrey Njoku, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a jihar Kano lokacin taron tattaunawa da manema labarai kan Sustainable Development Goals (SDGs).

A cewarsa, babban amfanin zuwa makaranta shine yaro ya iya karatu da lissafi na fari, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Hakazalika, Mr Rahama Farah, shugaban ofishin UNICEF dake Kano ya ce UNICEF da gwamnatin jihar Kano na hada kai wajen inganta ilmin Boko amma da sauran rina a kaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng