Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023

  • Myagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a garin Kiyawa
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Shisu, ya ce tuni kwamishina ya haɗa tawagar dakaru na musamman don ceto matar
  • A halin yanzun jami'an yan sandan sun fara aiki tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro da jama'ar gari

Jigawa - 'Yan bindigan sun sace mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanata na shiyyar jihar Jigawa ta tsakiya, Honorabul Tijjani Ibrahim Gaya.

Leadership ta ruwaito cewa matar ƴar kimanin shekara 70 a duniya, Hajiya Jaja, ta shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne a gidanta da ke ƙaramar hukumar Kiyawa, jihar Jigawa.

Yan bindiga sun shiga Jigawa.
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar dake arewa maso yammacin Najeriya, DSP Lawal Shisu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa maharan sun sace mahaifiyar ɗan takarar ne a farkon awannin ranar Talata, 21 ga watan Yuni, 2022, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da bayanin cewa maharan da ake zargin masu garkuwa ne sun farmaki gidan iyalan ɗan takarar Sanatan da ke garin Kiyawa kuma suka tilasta wa Dattijuwar tafiya tare da su.

Wane mataki yan sandan suka ɗauka?

A cewar kakakin yan sandan, bayan samun rahoton abun da ya faru, kwamishinan hukumar yan sanda ya shirya dakaru na musamman domin su bazama ceto matar.

Bugu da ƙari, DSP Shisu ya ce domin gaggauta ceto mahaifiyar jigon na APC, Dakarun sun haɗa guiwa da sauran hukumomin tsaro da sauran al'umma don samun sahihan bayanai.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa yan bindigan su 15 zuwa 20 suka shiga garin ɗauke da makamai a cikin Motoci, suka kutsa cikin gidan matar suka yi awon gaba da ita.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari kawo mutum 7 majalisa don su maye gurbin wasu ministocinsa

A wani labarin kuma Yan bindiga sun tayar da bama-bamai a wata babban kasuwa, sun yi mummunar ɓarna

Wasu tsageru da ake tsammanin mambobin IPOB ne sun ta da babbar kasuwar Izombe yayin da mutane suka fito kasuwanci a Imo.

Maharan da ake zaton masu ti l asta bin dokar zaman gida ne sun kona motoci biyu kuma suka jefa Bam a cikin kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262