Da Ɗumi-Ɗumi: Yan bindiga sun tayar da bama-bamai a wata babban kasuwa a Imo

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan bindiga sun tayar da bama-bamai a wata babban kasuwa a Imo

  • Wasu tsageru da ake tsammanin mambobin IPOB ne sun ta da babbar kasuwar Izombe yayin da mutane suka fito kasuwanci a Imo
  • Maharan da ake zaton masu tilasta bin dokar zaman gida ne sun kona motoci biyu kuma suka jefa Bam a cikin kasuwar
  • Yan kasuwan da suka fita don harkokin su na kasuwanci sun yi matuƙar firgita, wasu da dama kuma sun jikkata

Imo - A ranar Litinin wasu miyagun yan bindiga suka tada bama-bamai a Babbar kasuwar Izombe da ke ƙaramar hukumar Aguata, jihar Imo, yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Premium Times ta rahoto cewa ana zaton yan bindigan mambobin haramtacciyar ƙungiyar yan aware ne wato IPOB waɗan da ake zargin suna tilasta mutane bin dokar zaman gida kowace Litinin.

Taswirar jihar Imo.
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan bindiga sun tayar da bama-bamai a wata babban kasuwa a Imo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa tun farko maharan sun je kasuwar domin su gargaɗi mutane kar su yi yunkurin taka dokar ta hanyar fitowa kasuwanci, a ruwayar jaridar Sun.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Amma sai yan kasuwan suka yi kunnen uwar shegu da gargaɗin suka fito domin gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum, hakan ya tunzura yan ta'addan suka farmake su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ƙara da cewa sai da 'yan bindigan suka ƙone motocin biyo kafin daga bisani suka harba bama-bamai a harabar kasuwar.

Ya mutanen da ke kasuwanci suka yi?

Yan kasuwan da suka riga da suka fita gudanar da harkokin kasuwancin su sun firgita da harin, inda suka yi takansu domin tsira da rayuwarsu.

Wasu daga cikin yan kasuwan da dama sun jikkata yayin harin amma babu rahoton wani ya rasa rayuwarsa.

Wani shaidan da lamarin ya auku a kan idonsa ya shaida wa Jaridar cewa:

"Suna zuwa suka fara jefa Bam cikin kasuwar kuma nan take kowa dake ciki ya fara neman hanyar tserewa. Haka nan maharan sun zuba man Fetur kan wasu motoci biyu, ko ina da komai ya yi kaca-kaca a kasuwar."

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

A wani labarin kuma An gano gawar wata mata cikin yanayi a Abuja, wasu abu biyu na kusa da ita sun ɗaga hankulan mutane

Mutanen garin Kubwa a babbar birni n tarayya Abuja sun wayi gari ranar Litinin cikin tashin han kali.

Bayanai sun nuna cewa mazauna ƙaram in garin sun gan o gawar wata mata a juj i tare da gawarwaki biyu a kusa da ita cikin wani yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel