Yanzu-Yanzu: Mai Gari Da Dansa Da Aka Sace a Bauchi Sun Shaki Iskar Yanci Bayan Kwana 3 Hannun Yan Bindiga
Bauchi - Kwanaki uku bayan da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene suka sace su ba, Dagacin Kauyen Zira a karamar hukumar Toro, Yahaya Saleh Abubakar da dansa, Habibu Saleh sun samu yanci.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Kakakin yan sandan Jihar Bauchi SP Ahmed Wakili ya tabbatar da sakinsu yana mai cewa:
"Yau, Dagacin Kauyen Zira da dansa sun samu yanci kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, bai bada karin bayani ba dangane da sakinsu sai dai ya yi alkawarin zai bada bayani nan gaba idan ya samu.
Idan za a iya tunawa wasu yan bindigan ne suka sace dagacin da dansa sannan daga bisani suka nemi wani adadin kudi da ba a bayyana ba a matsayin fansa.
Ba a iya tabbatarwa ko an biya kudin fansar ba ko ba a biya ba.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng