Yan bindiga sun yi kazamin artabu da 'yan sanda a Zamfara, rai ya salwanta

Yan bindiga sun yi kazamin artabu da 'yan sanda a Zamfara, rai ya salwanta

  • Dakarun hukumar yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya a wata musayar wuta ta tsawon awanni
  • Kakakin yan sandan jihar, Muhammed Shehu, ya ce jami'an da haɗin guiwar yan bijilanti sun daƙile yunkurin kai hari wasu ƙauyuka biyu
  • Kwamishina ya yaba da jajircewar jami'an tsaron inda ya roke su da su cigaba da haka don kare rayuwar al'umma

Zamfara - Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ta ce dakarunta sun halaka ɗan bindiga ɗaya a wata musayar wuta da suka yi a ƙauyukan Gamawa da Unguwar Mata da ke ƙaramar hukumar Gummi.

A watan sanarwa da Channels TV ta ci karo da ita, kakakin hukumar yan sandan Zamfara, Muhammed Shehu, ya ce sauran 'yan bindigan sun tsere zuwa cikin jeji yayin fafatawar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari har cikin Masarauta, sun sace Mai Martaba Sarki a Arewa

Yan bindiga sun sake kai hari Zamfara.
Yan bindiga sun yi kazamin artabu da 'yan sanda a Zamfara, rai ya salwanta Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa jami'ai na musamman da aka girke a kan hanyar Gummi/Bukkuyum ne suka samu kiran gaggawa ranar Lahadi, inda aka sanar musu wasu yan bindiga a kan babura sun farmaki ƙauyukan da nufin kashe mutane.

Da yake bayanin yadda abun ya faru, Kakakin 'yan sandan Zamfara ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Jami'an yan sanda da haɗin guiwar yan Bijilanti a yankin da abun ya shafa sune suka haɗa kai suka tarbi yan ta'addan aka yi kazamar musayar wuta da ta shafe awanni."
"Sakamakon haka sun yi mummunan jikkata ɗan bindiga ɗaya yadda ba zai tsira ba, aka kwato Bindigarsa AK-47, yayin da sauran maharan suka ranta ana kare zuwa cikin jeji da raunukan harbi a jikkunan su."

Kwamishina ya yaba wa dakarun

Da yake martani game da nasarar, kwamishinan yan sandan Zamfara, Ayuba Elkana, ya yaba wa jajircewar haɗakar jami'an tsaron bisa nasarar da suka samu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Bauchi, sun aikata ɓarna sun sace Basarake da ɗansa

Ya kuma ƙara musu zumma da kada su kwanta bacci a kokarin da suke na tsare rayuka da dukiyar fararen hula na jihar baki ɗaya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Haka zalika kwamishinan ya umarci kwamandan Anka da DPOn da ke makwaftaka da shi, "Su girke ƙarin dakaru a cigaba da sintiri da shirin ko ta kwana don dakile yunkurin sake kai hari kauyukan da ke kusa."

"Haka nan su tabbata sun ceto mutum biyu da maharan suka tafi da su kafin isowar jami'an tsaro."

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari karamar hukumar gwamnan Bauchi

Yan bindiga sun kai harin yankin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi , arewa mas o gabashin Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun sun yi yunkurin sace mutane amma suka fuskanci turjiya daga matasa dole suka tsere daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262