Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ragargazar dukkan masu aikata laifuka a kasar nan
  • Ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci taron yaye daliban 'yan sanda a kwalejin horar da kwararrun jami'ai da ke Wudil a Kano
  • Shugaban ya kuma bukaci a samar da tsarukan da za su kawo sauyi tare da dakile aikata laifuka ta yanar gizo

Kano - A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce masu daukar doka a hannunsu, rike makamai ba bisa ka’ida ba da kuma cin gajiyar rashin tsoro za su fuskanci hukunci mai tsauri daga gareshi.

Ya yi jawabi ne a Wudil, Kano, a wajen bikin faretin yaye dalibai na kwas na hudu na makarantar ‘yan sanda ta Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Buhari zai dakile matsalolin tsaro
Shugaba Buhari: Sai na rukurkusa duk masu amfana da rashin tsaron kasar nan | Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna rashin amincewa da aikata munanan laifuka, inda ya bukaci ‘yan sanda da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansu na dakile 'yan ta'adda.

Ya kuma jaddada bukatar samar da manufofin yaki da laifukan yanar gizo da ka iya lalata muhimman ababen more rayuwa na kasa, da rage raunin kasa da dai sauran ababen da ba za a rasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Yanayin tsarin yau ya zarce kasa, ruwa, da iska, zuwa manyan yankuna na yanar gizo. Intanet da sabbin fasahohin zamni sun ba da dandamali ga laifuka masu tasowa da ke isa matakan da ba a taba gani ba.

Hakazalika, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, jami'an Najeriya za su wanzar da zaman lafiya a kasar.

A nasa bangaren, kwamandan makarantar, AIG AbdurRahman Ahmad, ya ce hukumar ta kara wa rundunar ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron kasar da jami’ai 1,748 baya ga 205 da aka yaye ta hannun shugaban kasa a ranar, inji rahoton Today.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.