Mai kwadayi ya san gidan mai rowa: An taso fasto Mbaka a gaba bisa kiran dan takarar shugaban kasa marowaci

Mai kwadayi ya san gidan mai rowa: An taso fasto Mbaka a gaba bisa kiran dan takarar shugaban kasa marowaci

  • Kalaman Fasto Mbaka da ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a matsayin ‘matashi mai tsananin rowa’ ya sha suka da caccaka
  • Mbaka ya ce Obi mutum ne da ba shi da karimci, ya kara da cewa kada 'yan Najeriya su zabi mutum mai makon jaraba
  • ‘Yan Najeriya sun yi ca a shafin Twitter inda suka bayyana shi a matsayin mai neman a bashi kudi kuma mai bibiyar 'yan siyasa.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shahararren limamin cocin Katolika, Ravaran, Father Ejike Mbaka na shan suka bayan kalaman da ya yi kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mbaka a yayin wani wa’azi ya bayyana Peter Obi a matsayin ‘matashi mai tsananin rowa’ inda ya bayyana cewa ba zai taba zama shugaban Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Faston da ya saba hasashen zabe ya ambaci ‘Dan takara 1 da ba zai kai labari a 2023 ba

Mbaka ya sha caccaka bisa sukar Peter Obi
Mai kwadayi ya san gidan mai rowa: An taso fasto Mbaka a gaba bisa kiran dan takarar shugaban kasa marowaci | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Abin da Mbaka ya fada game da Peter Obi

A wani rahoto da Legit.ng Hausa ta buga a baya, Mbaka ya bayyana cewa Obi mutum ne da ba shi da karimci, inda ya kara da cewa bai kamata a amince dashi ya zama shugaban kasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku ya nuna cewa a shirye yake ya ci zabe domin shi da Peter Obi ba sa takara tare yanzu.

‘Yan Najeriya sun caccaki Mbaka kan sukar Peter Obi

A halin da ake ciki dai, kalaman Mbaka kan Obi ya jawo cece-kuce, inda da yawa suka yi kaca-kaca dashi.

‘Yan Najeriya sun yi ta batutu a shafin Twitter inda suka caccaki Faston na Katolika wanda wasu ke bayyana shi a matsayin mai neman na aljihu da 'yan siyasa ke amfani dashi.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

@GideonFidy ya rubuta:

“Mbaka ya goyi bayan Buhari shugaban kasa mafi muni da aka taba yi saboda sun ba shi kudi, Mbaka ya goyi bayan Hope Uzodinma saboda ya samu kudi a wurinsa, ko da kai BH ne kawai ka ba shi kudi zai goyi bayanka. Babu wanda ke sake sauraransa."

@taqueenobi ya rubuta:

"Yayin da sauran bayin Allah ke karfafa zaben dan takarar da ya dace, Mbaka na neman wanda zai saye gobenmu da kudi. ABIN KUNYA."

@novieverest ne ya rubuta:

“Peter Obi bai ba Mbaka kudi ba a shekarun baya. Nuna min aikin da zan saka kudi a ciki kuma na sami sakamako. Abin da Peter Obi ya nema ke nan. Har yau Mbaka ya gaza hutawa."

Wani mai kuma @mrstanlei ya bayyana yadda yake mutunta babban limamin darikar Katolikan amma ya bayyana cewa ko da Paparoma Francis na birnin Vatican na Rome ba zai iya shawo kan shi kada ya zabi Peter Obi ba.

Kara karanta wannan

Arewa, da jerin kalubale 7 da suke jiran Peter Obi idan ya tsaya takarar Shugaban kasa

Faston da ya saba hasashen zabe ya ambaci ‘Dan takara 1 da ba zai kai labari a 2023 ba

A wani labarin, rabararen Ejike Mbaka wanda shi ne babban Limamin cocin Adoration Ministry da ke garin Eungu ya yi wani hasashe a game da zabe mai zuwa.

Rabararen Ejike Mbaka ya nuna cewa Peter Obi ba zai samu nasara a zaben 2023 ba. Rahoton nan ya fito daga gidan yada labarai na BBC Igbo a ranar Laraba.

Babban Faston ya ke cewa ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar LP matsolon mutum ne mai mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel