Katsina: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari, Sun Bi Gida-Gida Sun Sace Maza 6 Da Matar Aure Da Yarta
- Yan bindiga sun afka wa garin Shola da ke karamar hukumar Katsina a Jihar Katsina da hari a safiyar ranar Talata
- Majiya daga garin na Shola ta tabbatar da afkuwar harin, inda ta ce yan bindigan sun sace mutum takwas, shida maza da matar aure da yarta
- Shaidan gani da ido a garin ya ce yan bindigan da suka iso kan babura ba su kashe kowa ba ko raunata wani yayin sabon harin da suka kai
Jihar Katsina - Wasu yan bindiga sun kai hari a garin Shola a karamar hukumar Katsina ta Jihar Katsina, inda suka sace mutane takwas yayin harin.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Channels Television ta wayar tarho cewa yan bindigan a kan babura sun afka wa garin ne a safiyar ranar Talata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Channels Television ta lura cewa garin wanda ke bayan sabon ginin da aka mayar Asibitin Koyarwa Na Tarayya ta Katsina yana fuskantar barazana daga yan bindigan ne saboda kusancinsa a garin Bugaje a karamar hukumar Jibia inda yan bindiga suka yi kaka-gida.
Duk da cewa yan ta'addan ba su halaka ko raunata kowa ba a garin, wani ganau ya ce yan bindigan sun rika bi gida-gida, inda suka yi nasarar sace maza shida, matar aure daya da yar ta mai shekaru biyu.
Amma, Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ba ta riga ta tabbatar da afkuwar harin ba a lokacin hada wannan rahoton.
ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC
A wani rahoton, kwamitin Koli Ta Tsaro a Najeriya, NSC, ta ce Kungiyar Ta'addanci Ta ISWAP ce ta kai harin da aka kai a cocin St Francis da ke Owo, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane 38 a ranar 5 ga watan Yunin 2022, Channels TV ta rahoto.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai na gidan gwamnati jawabi bayan taron Kwamitin Kolin Tsaro a Abuja.
Ya bayyana cewa an umurci jami'an tsaro, musamman yan sanda su kama wadanda suka aikata laifin.
Tsohon gwamnan na Jihar Osun ya ce harin ba ta da alaka da addini ko kabilanci, yana mai tabbatar da cewa hare-haren kungiyar ba ta da alaka da addini.
Asali: Legit.ng