'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Coci, Sunyi Awon Gaba Da Masu Ibada a Ogun

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Coci, Sunyi Awon Gaba Da Masu Ibada a Ogun

  • Wasu yan bindiga sun kai hari wani coci a karamar hukumar Ewekoro na Jihar Ogun a daren ranar Litinin sun sace masu ibada
  • Wani jami'in cocin Oluwatomisin Ehuwaojomo, a ranar Talata ya tabbatar da harin yana mai cewa maharan sun nemi N50m a matsayin kudin fansa
  • Ehuwaojomo ya ce ya shaida wa yan bindigan cewa shi Ubangiji ya ke yi wa hidima kuma baya karbar albashi amma ya sanar da kwamishinan yan sanda

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa cocin 'Celestial Church-Christ, SBJ Oshofa a Wasimi, karamar hukumar Ewekoro na Jihar Ogun, sun sace masu ibada biyu.

Wadanda aka sace din sun hada da wani ma'aikacin cocin Oluwaseun Ajose da wani malamin da ke koyarwa a cocin, Dagunro Ayobami.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun yi Garkuwa da Mata 2 a Konduga, Kwamishinan 'Yan Sanda

Yan bindiga sun sace masu ibada a cocin Ogun.
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Afka Coci a Ogun, Sunyi Awon Gaba Da Masu Ibada.@Vanguardngr.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan su hudu, sun afka cocin misalin karfe 11 na daren ranar Litinin, suka sace masu ibadan su biyu.

Wata majiya ta ce cocin yana wani wuri ne kebabbe, hakan yasa yan bindigan suka iya kai harin ba tare da an dakile su ba.

An tattaro cewa tawagar hadakar jami'an tsaro da yan vigilante sun fara bincika dazuka domin nemo wadanda aka sace.

Wani jami'in cocin, Oluwatomisin Ehuwajaojomo, a ranar Talata ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya kuma tabbatar cewa masu garkuwar sun tuntubi cocin suna neman a biya su N50m a matsayin kudin fansa.

Ehuwaojomo ya ce:

"Lokacin da mataimaki na ya kira ni kimanin awa biyu bayan sun tafi, masu garkuwan da farko sun ki magana da ni amma a karo na uku, sun yi magana da ni sun kuma nemi N50m kudin fansa.

Kara karanta wannan

Yan Bindigan Da Suka Sace Shugaban CAN a Plateau Sun Bayyana Kudin Da Za A Biya Don Fansarsa

"Na fada musu, ni Ubangiji na ke yi wa hidima kuma bana karbar albashi. Na yi magana da kwamishinan yan sanda, suna daukan mataki kan lamarin."

Yan sanda sun yi martani

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ba a yi masa bayani game da afkuwar lamarin ba.

Amma, ya yi alkawarin zai tuntubi wakilin mu idan ya samu bayani.

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Bi Shugaban CAN Har Gida Sun Sace Shi a Plateau

A wani rahoton, Yan bindiga sun sace limamin cocin Katolika na St Anthony a garin Angware a karamar hukumar Jos, Rabaran James Kantoma, wanda kuma shine shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, a karamar hukumar.

The Punch ta rahoto cewa an sace Kantoma a gidansa da ke garin a daren ranar Lahadi.

Wani mazaunin garin Angware, Silas Joshu, ya tabbatar wa The Punch da sace malamin addinin a Jos a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel