Innalillahi: Allah ya yiwa fitaccen basaraken gargajiya, Maiyaki na Kupa rasuwa
- A yau ne muke samun labarin rasuwar basaraken gargajiya a jihar Kogi, Alhaji Muhammadu Kabir Isa (II)
- An ruwaito cewa, Allah ya yiwa Maiyaki rasuwa ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani asbiti mai zaman kansa
- Rahoto ya bayyana yadda ya yi rayuwarsa, da kuma irin tasirinsa a cikin al'ummar Kogi da kuma Nupe a yankinsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Neja - Maiyaki (Estu) na Kupa, Alhaji Mohammadu Kabir Isah (11), mai kula da garin Kupa ya rasu bayan ya kwashe sama da shekaru 42 akan karagar mulki.
Ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Bida, babban birnin jihar Neja a ranar Lahadi 12 ga watan Yuni, Daily Trust ta ruwaito.
Marigayi sarki ya zama sarkin gargajiya na Kupaland a ranar 2 ga Oktoba, 1979.
Har zuwa rasuwarsa, ya kasance mataimakin shugaban majalisar gargajiya ta Lokoja kuma mai kula da al’adun mutanen Kupa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Marigayin sarkin gargajiya ne da ake girmamawa a lardin Nupe kuma babban mashawarci ne ga Sarkin Bida, Etsu Nupe.
Maiyaki na Kupa Alhaji Muhammadu Kabiru Issa (II) yana cikin sarakunan gargajiya da aka daga darajarsu zuwa matakin farko shekaru uku da suka wuce.
Ya karbi sandarsa ta aiki daga Gwamna Yahaya Bello.
Ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya, jikoki, da sauran dangi, daga cikin su akwai Ambasada Adamu Isa, Dauda Kabir Isa, masanin harhada magunguna; Malam Umar Kabir Isa, Hauwa Isa, Hajara Isa da Malam Abdulmalik Suleiman, inji This Day.
Tuni dai aka yi jana’izarsa a garin Abugi Kupa da ke karamar hukumar Lokoja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Allah ya yiwa wani tsohon sanatan Najeriya rasuwa
A wani labarin, dan siyasar jamhuriya ta biyu, Sanata Francis Arthur Nzeribe, haifaffen garin Oguta, ya rasu yana da shekaru 83.
Wata majiya mai karfi ta kusa da danginsa da ta zanta da jaridar Punch tare da neman a boye sunanta da yammacin ranar Lahadi ta ce dan siyasar ya mutu ne a wani asibiti a kasar waje.
Iyalan sun tabbatar da mutuwar dan siyasar a wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Asali: Legit.ng