An Kama Mafarauta 3 Kan Zargin Garkuwa Da Mutane a Adamawa
- Yan sanda a Jihar Adamawa sun yi nasarar kama wasu mafarauta uku da laifin garkuwa da mutane a kananan hukumomin Girei da Fufore na jihar
- SP Sulaan Nguroje, mai magana da yawun yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da hakan ya ce an kwato bindiga da wasu abubuwan a hannunsu
- Nguroje ya ce binciken da aka fara yi a farko ya nuna cewa mutanen ukun sun ci amanar da aka dora musu suka koma hada baki da masu garkuwa suna kai musu abinci da wasu abubuwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Adamawa - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Adamawa ta kama mafarauta uku da wasu kan hadin baki don garkuwa da mutane a kananan hukumomin Girei da Fufore a jihar, Daily Trust ta rahoto.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Sulaan Nguroje, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce wadanda ake zargin:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Auwal Muhammad mai shekara 28, Isa Umaru dan shekara 40, da Rabiu Mohammed dan shekara 19 an kama su suna addabar kauyukan Pariya Daware da Girei."
Ya kara da cewa yan sandan sun kwato babur guda daya da bindiga pistols wanda aka kera a Najeriya da wasu kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin.
"Binciken da aka yi kawo yanzu ya nuna wadanda ake zargin sun ci amanar da aka basu na tsare rayuka da dukiyoyin al'umma, suke yi wa masu garkuwa safarar abinci da wasu kayayyaki a yankin," in ji sanarwar.
'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci
A wani rahoton, rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.
Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare
A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.
Kamar yadda takardar tazo:
“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”
Asali: Legit.ng