Asirin ‘Yan ta’adda ya tonu, Dakarun Sojoji sun bankado shirin hare-haren da za a kai
- Shugaban hafsoshin tsaro na kasa ya ce sojoji sun bankado ta’adin da ‘yan bindiga suke shiryawa
- A makon da ya gabata an yi kokarin kai hare-hare a wasu garuruwa, daga ciki har da birnin Abuja
- Sojoji ne suka yi ta-maza, suka hana miyagu kai hari a Kano kamar yadda aka gani a jihar Ondo
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - A ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni 2022, shugaban hafsoshin tsaro na kasa, Janar Lucky Irabor, ya ce sojoji sun datse shirin harin ‘yan ta’adda.
Daily Trust ta rahoto Janar Lucky Irabor, yana mai cewa ‘yan ta’adda sun yi niyyar kai hari a Abuja da wasu manyan biranen a makon da ya gabata.
Duk da an hallaka mutane 40 a wani coci da ke garin Owo a jihar Ondo, babban hafsun sojojin ya ce ba don namijin kokarinsu ba, da ta’adin ya zarce haka.
Janar Irabor yake cewa ‘yan ta’adda sun nemi a kai makamancin harin da aka kai a Ondo a jihar Kano. A karshe dai an yi nasarar hana aukuwar wannan.
Rahoton ya ce sojan ya yi wannan bayani ne da aka yi hira da shi a wani shiri da aka yi a kan ranar damukaradiyya a gidan talabijin nan na Channels TV.
Yadda rundunar sojoji suka iya bankado mugun nufin da ‘yan ta’adan shi ne tun wuri sun gano IED wanda ake amfani da su wajen hada bama-bamai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun gano tulin makamai da harsashe da wasu kayan da ‘yan ta’adda suka nemi su yi amfani da su a bangarorin kasar nan, har da birnin Abuja.”
“Watakila ba ku sani ba, a makon da aka kai harin Owo, misali a Kano, jami’an tsaro sun samu bayanan sirri, aka hana aukuwar babbar musiba.”
- Janar Lucky Irabor
Duk da kashe-kashen da ake fama da shi, babban jami’in sojan ya ce ana ganin cigaba a harkar tsaro.
Irabor yake cewa daga shekarar bara zuwa yanzu, an samu saukin ta’adin da ake yi daga duka yankunan Arewa zuwa bangarorin kudancin Najeriya.
Rahoton ya ce Hafsun ya roki mutanen Najeriya su zama sun yi imani da jami’an tsaro domin ganin an yi nasara a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a kasar.
Siyasar 2023
Idan aka koma fannin siyasa, za a ji labari APC ta rasa Kiristan da za ta dauko daga Arewacin Najeriya, za ta iya jarraba takarar Musulmi da Musulmi a 2023.
Haka zalika a PDP, mataimakin Atiku Abubakar zai iya zama tsakanin Gwamna Ifeanyi Okowa, Gwamna Udom Emmanuel da kuma Gwamna Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng