Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 74, an sako mutum 11 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
- An yi musayar fursunonin farko tsakanin gwamnatin tarayya da yan ta'addan Ansaru da suka kai hari jirgin kasa
- Tukur Mamu, ya sanar da cewa an sako mutum goma sha daya cikin fasinjoji 62 da aka sace a jirgin kasan
- Yan bindigan sun bukaci a saki 'yayansu takwas kafi su saki wasu daga cikin fasinjojin da suka sace
Jihar Kaduna - Yan ta'addan da suka kai har jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sako wasu daga cikin mutum sama da sittin da suka kwamushe ranar 28 ga Maris, 2022.
Mai gidan jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya bayyana hakan yace mutum goma sha daya (11) aka sako ranar Asabar, 11 ga Yuni, 2022., rahoton Daily Trust.
A cewarsa, cikinsu akwai mata shida da maza biyar.
Amma yace majiyoyinsa suna mazajen da aka saki na fama da rashin lafiya ne yayinda matan da aka sake marasa karfi ne kamar yadda akayi yarjejeniya da yan bindigan.
Yace:
"Abinda aka sa rai dama shine su saki dukkan matan da suka sace a karon farko amma sai suka rage adadin matan da zasu saki saboda gwamnatin Najeriya ta bukaci a saki masu jinya."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar 28 ga watan Maris ne 'yan ta'addan suka halaka fasinjoji tara gami da garkuwa da mutane da dama bayan lalata jirgin kasa a wani kilomita kadan daga Kaduna, babban birnin jihar Kaduna. Daga bisani sun sako wasu daga ciki, tare da barin 62 a hannunsu.
An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji
'Yan ta'addan sun kara sati biyu a kan wa'adin barazanar halaka fasinjoji 62 da har yanzu suke hannunsu.
Zaku tuna cewa sharadin da yan bindiga suka bada shine Wajibi ne gwamnatin tarayya ta sakar musu yaransu takwas dake hannunsu kafin ko ranar 13 ga watan Juni daga nan ne za a cigaba da maganar sakin fasinjoji 62.
Mamu ya ce ya yi nasarar rarrashin 'yan ta'addan har suka jinkirta wa'adin kwanakin da suka bayar bayan an gano inda yaran nasu suke tare da taimakon hukumomin tsaro na jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng