N20,000 muke dayan rigar Soja, N370,000 muke sayan bindiga : Yan bindiga

N20,000 muke dayan rigar Soja, N370,000 muke sayan bindiga : Yan bindiga

Jos - Jami'an sashen leken asiri na hukumar yan sanda FIB-IRT sun damke yan bindiga masu garkuwa da mutane 14 da aka dade ana nema ruwa a jallo a Arewacin Najeriya.

Cikin yan bindigan akwai masu sayar da makamai da masu yiwa yan matan da suka sace fyade, rahoton Vanguard.

Hakazalika sun bayyana yadda suke sayan rigar Sojojin da suke amfani da kuma wajen wadanda suke saya.

Plateau
N20,000 muke dayan rigar Soja, N370,000 muke sayan bindiga : Yan bindiga
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin bincike daya daga cikinsu mai suna Abubakar, ya bayyana cewa wani Iliyasu Saidu a.k.a Yellow da Sky Brother ne suka shigar da shi harkar.

Ya bayyana sunayen wasu mambobin kungiyar garkuwa da mutanen da suke aiki tare a garn Bokkos, jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

A cewarsa akwai Iliyasu Saidu (a.k.a. Yellow), Badamosi Ardo Yakubu, Sky Bokkos, Zaki Bokkos, Yakubu Joshua Bokkos da Annas Iliya

Yace:

"Na yi fashi da makami sau tari a kauyukan Bokkos, Mangu da Jos. Muna da bindigogi AK47 guda shida, kuma man amfani da kayan Sojin da muke saya wajen wani IK a garin Daffo N20,000. Hakazalika muna da telan dake dinka mana a Bokkos."
"Muna da mai kawo mana makami. Sunansa Ali Ibrahim. Na sayi AK 47 wajensa N370,000. Harsasai kuma wani Yakubu Joshua na sayar mana guda 30 kudi N30,000."

Asali: Legit.ng

Online view pixel