Idan Tinubu ya zabi Musulmi yayi masa mataimaki babu komai za muyi biyayya: Fani-Kayode

Idan Tinubu ya zabi Musulmi yayi masa mataimaki babu komai za muyi biyayya: Fani-Kayode

  • Femi Fani Kayode ya yi amai ya lashe, yace duk wanda Tinubu ya zaba zasu goyi bayansa
  • Kayode wanda ya koma jam'iyyar APC kwanaki yace har yanzu yana kan bakarsa ba za'a iya raba addini da siyasa ba amma zai yi biyayya idan aka zai Musulmi
  • Jam'iyyar APC ta shiga tsaka mai wuya wajen zaben wanda zai zama mataimakin Tinubu a zaben 2023

Abuja - Tsohon Ministan Sufurin sama, Femi Fani-Kayode yace zai goyi bayan dan takaran shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, koda ya zabi mataimaki Musulmi.

Kayode ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV ranar Alhamis.

Yace sam ba zai yiwu ace za'a cire addini daga cikin siyasa.

Yace:

"Matsala ne kuma wajibi ne mu yiwa mutane bayani idan muka yanke shawarar yin haka. Ba ni da matsala idan aka yi haka (Musulmi da Musulmi). idan dan takara ya zabi hakan zamu goya masa baya."

Kara karanta wannan

Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i

"Amma muna bukatar kare abinda muka zaba. Ba zai yiwu muce babu addini cikin siyasar yau ba. Musamman yanzu da aka kashe Kirista 50 a Coci a Owo kuma a Kaduna aka kashe Kirista 34."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fani-Kayode
Idan Tinubu ya zabi Musulmi yayi masa mataimaki babu komai za muyi biyayya: Fani-Kayode Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Fani-Kayode a karshe yace koda APC ta zabi Musulmu matsayin mataimaki, za goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu.

Cikin wadanda ake hasashen Tinubu zai zaba sune Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Kaduna, Nasir E-Rufa'i; Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi Alla-wadai da yadda mutane ke damun kansu kan maganar daukan Musulmi ya zama mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin hira a ChannelsTV ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

N20,000 muke dayan rigar Soja, N370,000 muke sayan bindiga : Yan bindiga

Ya bayyana cewa mutumin kwarai ake bukata ya zama abokin tafiyar Tinubu kuma addininsa ba shi muhimmanci.

Bamu yarda Musulmi da Musulmi su zama Shugaba da mataimaki ba: Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta gargadi jam'iyyun siyasa kada suyi kuskuren zaben Musulmi da Musulmi matsayin yan takaran Shugaban kasa da mataimaki a 2023.

Sakataren kasan na kungiyar, Joseph Bade Daramola, ya bayyana hakan ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja, rahoton DailyTrust

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng