'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya
- Wasu miyagun yan bindiga sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun aikata babbar ɓarna
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun sace shugaban matasan yankin, yayin da suka haɗa da Motoci masu tsada
- Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra ya ce har yanzun ba su samu rahoton faruwar lamarin ba
Anambra - Yan bindiga sun yi awon gaba da wani shugaban matasa a ƙaramar hukumar Ihialia da ke jihar Anambra, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wata majiya a yankin ta bayyana cewa bayan sace shugaban matasan, maharan sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukuma suka kwashi motoci masu darajar miliyoyin kuɗi da aka tanada son tallafawa mutane.
Shugaban ƙungiyar cigaban matasa ta Okija, Kwamaret Ononuju Maxwell Chigozie, a wata sanarwa ya ce mazauna yankin sun shiga ƙunci sanadiyyar harin.
A cewarsa, Honorabul Chuddy Ifeanyi Momah, shi ya aje motocin da maharan suka sace da nufin rabawa mutanen mazaɓar ƙaramar hukumar Ihiala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa ɗan majalisar tarayyan ya aje motocin ne yana jiran lokacin da ya dace ya rabawa mutanen mazaɓarsa da niyyar taimaka musu kafin lamarin ya faru.
A jawabinsa shugaban ƙungiyar matasan ya ce:
"Maganar gaskiya mummunan lamarin ya auku ne da tsakar dare, a lokacin suka tasa shugaban matasan mu, suka tilasta masa ya nuna musu inda aka aje motocin waɗan da sun kai darajar miliyan N50m."
Bamu da rahoto - Yan Sanda
Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce rahoton garkuwa da shugaban matasan da sace motocin be zo ofishin yan sanda ba.
Kakakin yan sandan ya roki waɗanda harin ya shafa da mutanen da suka shaida abun da idon su, su gaggauta kai rahoto ofishin yan sanda mafi kusa domin taimaka wa hukumar ta gudanar da aikinta.
Da Dumi-Dumi: Sawore ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a AAC, zai gwabza da Atiku, Tinubu
A wani labarin kuma Hukumar Hisbah ta kama wani mutumi da ya gina gida da shafukan Alƙur'ani, ya faɗi Malamin da ya ba shi Fatawa
Hukumar Hisbah mai kokarin tabbatar da Shari'ar Musulunci a Kano ta kama wani mutumi bisa zargin gina gida da shakukan Alkur'ani.
Mataimakin kwamandan Hisbah, Ustaz Usaini Usman, ya ce dakaru sun kamo mutumin tare da malamin da ya ba shi fatawa.
Asali: Legit.ng