Dirama yayin da ɗan sanda ya fallasa yadda wani Mahaifi ke saduwa da 'ya'yansa mata biyu ba kunya

Dirama yayin da ɗan sanda ya fallasa yadda wani Mahaifi ke saduwa da 'ya'yansa mata biyu ba kunya

  • Jami'in hukumar yan sanda mai gabatar da ƙara ya shaida wa Kotun Majirtire a Legas yadda wani Magidanci ke kwanciya da yayansa mata
  • Ɗan sandan, Lucky Ihiehie, ya ce magidancin ɗan shekara 58 ya fara saduwa da yaran biyu ne tun shekaru biyu da suka gabata
  • Bayan sauraron duk abin da ya faru, Alkalin Kotun ta ɗage zaman har zuwa lokacin da za'a ji shawarin sashin DPP

Lagos - An kalli wata Dirama a Kotun Majistire a jihar Ƙegas lokacin da ɗan sanda ya yi bayanin yadda wani magidanci ɗan shekara 58, Shola Jolaosho, ya ke Jima'i da ƴaƴansa mata biyu.

Daily Trust ta rahoto cewa matan biyu na da shekara Tara da kuma babban yar kimanin shekara 13 a duniya kuma mutumin ne mahaifin su na jini.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da Jami'an tsaro mata biyu suka buɗa, suka ba hammata iska a filin taron APC

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya ce wanda ake zargin, mahaifin yaran mata biyu, ya fara saduwa da su ne shekara biyu da suka gabata kuma ya yi ikirarin cewa sharrin sheɗan ne lokacin da asirinsa ya tonu.

Bajen hukumar yan sanda.
Dirama yayin da ɗan sanda ya fallasa yadda wani Mahaifi ke saduwa da 'ya'yan mata biyu ba kunya Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Mai gabatar da ƙara na hukumar yan sandan ya shaida wa Kotu cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai shari'a, tun da har wanda ake zargin ya ce sheɗan ne ya rinjaye sa ya ke aikata haka, yana nufin suna aiki tare da Sheɗan lokaci zuwa lokaci, ka tura shi gidan Yari domin ya zama cikakken ma'aikacin sheɗan."

Rahoto ya nuna cewa wanda ake zargin mazaunin Layin Fadare da ke Ogba a jihar Legas, yana amfani da lokacin da matarsa ta fita Anguwa ya ci zarafin 'ya'yan mata.

Ɗan sandan ya kara da cewa Magidanci, a duk lokacin da ya kwanta da su, yana musu barazana mai tsoratarwa matukar suka tona masa asiri ga kowa, har da mahaifiyar su.

Kara karanta wannan

NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida

Ta ya asirin mutumin ya tonu?

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Lucky Ihiehie, ya cigaba da cewa:

"Babbar ɗiyar ce ta sanar da mamarsu abinda ke wakana yayin da ta ji ba zata iya cigaba da jure lamarin ba, wanda hakan ya sa aka kama shi."
"Da farko ya musanta kwanciya da yaran, amma sai ya ɓarke da kuka lokacin da aka kawo masa babbar ɗiyarsa yar shekara 13."

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alƙalin Kotun, Mai Shari' Misis O. A. Layinka, ta ba da umarnin a cigaba da tsare mutumin kuma ta ɗage zaman domin jiran shawarin sashin hukunta masu aikata manyan laifuka (DPP).

A wani labarin na daban kuma Daga karshe, Shugaba Buhari ya magantu kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC

Shugaba Buhari ya yi magana kan nasarar Tinubu, ya ce shi ne ɗan takarar da ya dace ya karɓi Najeriya a 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya magantu kan kowane ɗaya daga cikin yan takara 5 da gwamnoni suka kai masa

Sai dai shugaban kasan ya gar g aɗi jam'iyyar APC cewa dole kowa ya ma ida wuƙarsa kube, a haɗa kai don tunkarar zaɓe don cin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262