NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida

NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida

  • Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar gwamnan Kano a NNPP ya ce idan ya zama gwamna zai maida hankali kan yaƙi da cin hanci
  • Ɗan takarar kuma surukin Sanata Kwankwaso, ya ce duk lalacewar da Kano ta yi idan ya zama gwamna komai zai zama tarihi
  • A wani ɓangaren kuma, ɗan takarar NNPP a zaɓen gwamnan Oyo, ya ɗauƙi alƙawurra idan har mutanen jihar suka zaɓe shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Ɗan takarar gwamna karkashin inuwar NNPP a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa yaƙi da masu cin hanci da rashawa zai zama ɗaya daga cikin abun da zai yi yaƙin neman zaɓe da shi.

Ɗan takarar wanda ya shahara da sunan Abba Gida-Gida ya ce da zaran ya karɓi mulkin Kano masu cin hanci sun shiga uku, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC

Abba ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga dubbannin magoya bayansa da suka taru a cibiyar Abacha Youth Centre a Kano domin tabbatar masa da takara.

Abba Kabir Yusuf.
NNPP 2023: Da zaran na zama gwamnan Kano masu cin hanci sun shiga uku, Abba Gida-Gida Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kuma ɗauki alkawarin inganta aikin gwamnati ta hanyar ba da horo, ƙara wa ma'aikata matsayi, ɗaukar sabbin ma'aikata da kuma biyan albashi da Fansho a kan lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sabuwar sanarwa da aka rabawa manema labarai, Kakakin ɗan takaran, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Uban gidansa ya shirya gyara jihar Kano zuwa hanya mai kyau.

"Muna fatan cimma haka ne ta hanyar jawo kowa a jiki wajen tafiyar da gwamnati," a cewar Bature.

NNPP a jihar Oyo

Haka nan kuma, ɗan takarar gwamnan Oyo na jam'iyyar NNPP, Popoola Olukayode Joshua, ya tabbatar wa mutane cewa zai fifita tsaro, ilimi, tattalin arziƙi, lafiya da sauran muhimman abubuwa idan suka zaɓe shi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar NNPP ta sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan Katsina

Ya ce tsarin NNPP na da ƙarfi a dukkan gundumomi 351 na jihar Oyo, inda ya ƙara da cewa jam'iyyar zata ci nasara da tazara mai ɗumbin yawa.

A wani labarin kuma Bayan zaftare yan takara zuwa biyu, An matsawa Osinbajo ya janye don tabbatar da magajin Buhari

Yankin kudu maso yammacin Najeriya na kokarin ganin an kawo karshen rikicin neman tikitin takarar shugaban kasa a APC .

Wasu bayanai sun nuna cewa yan takara sun zama biyu, kuma Sarakuna sun matsawa Osinbajo lamba ya janye wa Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel