Yanzu-Yanzu: ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC

Yanzu-Yanzu: ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce yan kungiyar ta'addanci na ISWAP ne suka kai hari a cocin Owo a jihar Ondo suka kashe masu Ibada su 38
  • Rauf Aregbesola, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Laraba bayan taron NSC
  • Aregbesola ya ce gwamnati ta umurci yan sanda da sauran jami'an tsaro su tabbatar sun kamo wadanda suka kai mummunan harin domin su fuskanci hukunci

FCT, Abuja - Kwamitin Koli Ta Tsaro a Najeriya, NSC, ta ce Kungiyar Ta'addanci Ta ISWAP ce ta kai harin da aka kai a cocin St Francis da ke Owo, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane 38 a ranar 5 ga watan Yunin 2022, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na jagorantar zaman shawo kan matsalar tsaro

Yanzu-Yanzu: ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC
NSC: ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo. Hoto: @Channelstv.
Asali: Twitter

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai na gidan gwamnati jawabi bayan taron Kwamitin Kolin Tsaro a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An umurci jami'an tsaro su kai harin

Ya bayyana cewa an umurci jami'an tsaro, musamman yan sanda su kama wadanda suka aikata laifin.

Tsohon gwamnan na Jihar Osun ya ce harin ba ta da alaka da addini ko kabilanci, yana mai tabbatar da cewa hare-haren kungiyar ba ta da alaka da addini.

A cewarsa, NSC din ta damu da kashe-kashe da ake yi da sunan batanci kuma ta umurci hukumomin tsaro su binciko wadanda ke da hannu kan hakan musamman a Jihar Sokoto da Birnin Tarayya Abuja.

Wadanda suka hallarci taron tsaron

Wadanda suka hallarci taron tsaron sun hada mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau

Babban hafsin tsaro, Janar Lucky Irabor; Babban hafsan sojojin kasa, Lt Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao suma sun hallarci taron.

Sufeta Janar na Yan sanda, Alkali Usman, Shugaban SSS, Yusuf Bichi; da Shugaban NIA, Ahmed Abubakar suna wurin taron, Punch ta rahoto.

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

A wani rahoton, Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda zasu cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Gwamnan ya kwatanta tubar mayakan Boko Haram da ISWAP fiye da 35,000 a matsayin taimako daga Ubangiji sakamakon addu’o’in mutane daban-daban na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164