Adamawa: Gwamna Fintiri ya saka dokar hana fita a kananan hukumomi biyu
- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya saka dokar zaman gida a kanann hukumomi biyu na jihar
- Gwamnan ya ce gwamnati ba ta da wani zaɓi biyo bayan ƙara ruruwar wutar rikicin kabilanci a yankunan da wasu sassan Gombe
- Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce ta baza komarta ko ina a yankin don kama bara gurbin da basu kaunar zaman lafiya
Adamawa- Domin daƙile yaduwar rikicin kabilanci da ya ƙi ya ƙi cinyewa a wasu yankunan da ke da iyaka tsakanin jihar Adamawa da Gombe, Gwamna Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita a kananan hukumomi biyu.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa dokar hana fitan ta shafi kananan hukumomin Lamurɗe da Guyuk a jihar Adamawa.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙara ruruwar wutar rikici tsakanin kabilar Wajas da Lugundas a yankunan waɗan nan kananan hukumomin da wasu sassan Gombe.
Yayin nuna damuwa da takaicin kan cigaba da samun arangama tsakanin al'ummomin biyu, gwamna Fintiri ya yi gargaɗi da cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Wasu bara gurbi na kokarin kai gwamnati bango saboda haka a shirye muke mu yi duk me yuwuwa wajen kawo karshen lamarin."
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Humashi Wunoshikou, ya fitar ya ce:
"Mun baza komar mu ta ko ina don kama duk wasu marasa ji a yankin kuma ba mu da wani zaɓi da ya zarce mu kawo ƙarshen wannan rikicin ta kowace hanya."
Gwamnan ya ƙara da cewa abun takaici ne da dana sani duba da abubuwan da ke faruwa, gwamnati ba ta da wani zaɓi da ya wuce ƙaƙaba dokar zaman gida.
Me dokar hana fitan ta ƙunsa?
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa gwamnati na da masaniyar wasu tsiraru na shirin ɗaukar doka a hannu ta hanyar farmakan mutane a cikin gidajen su da wuraren ayyukan su.
A ruwayar Daily Trust dokar zata yi aiki ne daga ƙarfe 5:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe har zuwa sanda gwamnati zata waiwaye ta.
"Biyo bayan cigaba da samun rikici a wasu yankunan kananan hukumomi biyu, Lamurɗe da Guyuk, gwamna Ahmadu Fintiri ya saka dokar hana fita a a garuruwan Lafiya da Boshikiri."
"Haka nan dokar zata shafi kauyukan da ke zagaye da waɗan nan garuruwan kamar Mumseri, Mere, Kupte da Zakawon, dokar zata fara aiki nan take."
A wani labarin kuma Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malamai su koma aiki
Gwamnatin jihar Edo ta dakatar da ayyukan dukkan wasu ƙungiyoyi da suka shafi manyan makarantun gaba da Sakandire mallakin jiha.
Gwamnatin karkashin gwamna Godwin Obaseki ta ce duk wani ma'aikaci da yaƙi bin umarni zata sallame shi daga aiki.
Asali: Legit.ng