Gabanin zaben 2023: Tashin hankali zai kunno kai a fadin kasar, inji Babban Hafsan Sojoji

Gabanin zaben 2023: Tashin hankali zai kunno kai a fadin kasar, inji Babban Hafsan Sojoji

  • Abubuwa na iya tabarbarewa a Najeriya yayin da ake shirye-shiyen babban zaben 2023 da ke kara gabatowa
  • Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Faruk Yahaya ne ya yi wannan gargadi a lokacin da yake jawabi ga Kwamandojin sojoji a jihar Rivers
  • Yahaya ya yi hasashen cewa wasu yan siyasa na iya daukar yan baranda don kawai su cimma manufofinsu na son zuciya

Rivers - Gabannin babban zaben 2023, Shugaban hafsan soji na kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya yi hasashen wasu lamura da ka iya tasowa daga bangaren siyasar kasar.

Yahaya ya bayyana cewa abubuwa na iya tabarbarewa a bangaren siyasa a fadin yankunan kasar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni a Port Harcourt, da yake jawabi a wani taron kwamandojin rundunar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Gabanin zaben 2023: Tashin hankali zai kunno kai a fadin kasar, inji Babban Hafsan Sojoji
Gabanin zaben 2023: Tashin hankali zai kunno kai a fadin kasar, inji Babban Hafsan Sojoji Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shugaban sojin ya gargadi dakarun rundunar da su guji shiga harkar siyasa yayin da zaben 2023 ke gabatowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babu jami’in da za a bari ya shiga harkar zaben ko kuma ya marawa wani dan takara baya kamar yadda yake bisa dokar aikin.

Jaridar The Nation ta nakalto Yahaya yana cewa:

“Saboda haka, Ina so na tunatar da dukkanin kwamandoji cewa yayin da lokacin zabe ya gabato akwai yiwuwar bangaren siyasar ya yi tsami a fadin yankunan kasar.
“Hada kai da yan dabar siyasa; amfani da kalaman kiyayya da sauran abubuwa marasa amfani daga bangaren yan siyasa masu son zuciya da magoya bayansu zai iya haifar da rashin tsaro a cikin kwanaki masu zuwa.
“Ina umurtan kwamandoji a dukkan matakai da su tabbatar da ganin cewa an wayar da kan dakarun rundunar yadda ya kamata kan kauracewa siyasa da nisantan duk wani rikici na siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Martanin dan takarar Osinbajo bayan shan kaye a zaben fidda gwanin APC

“Da wannan, ya zama dole dukkanin Jami’an soji su yi aiki bisa iyakar doka; su bi tsarin da aka shimfida na aiki da ka'idojin gudanarwa na zabe a 2023.”

Yahaya ya ce rundunar za ta yi amfani da tsarin aiki mai tsauri da amfani da karfin hadin gwiwa na dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a cikin kwanaki da makonni masu zuwa.

Ya ce an shirya taron ne don karawa juna sani da kuma samar da mafita mai dorewa kan kalubalen da ke fuskantar ayyukan da ke gudana a kasar.

An yi kutse a shafin NNPC na Twitter, an yi amfani da shi wajen hasashen abokin takarar Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa shafin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni, ya wallafa wani sako game da abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

Tinubu ya samu kuri’u 1,271 wajen kayar da sauran abokan karawarsa a zaben fidda gwanin APC wanda aka kammala a ranar Laraba.

Rotini Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma babban abokin karawarsa, ya samu kuri’u 316 yayin da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 235.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng