Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci
- Rundunar yan sanda a birnin tarayya Abuja ta ce sunan mutumin da fusatattun matasa suka kashe kan batanci, Ahmad Usman
- Rundunar ta ce abin da ta gano shine cacar baki ya shiga tsakanin Usman da wani malami a unguwar kuma malamin ya taro mutane suka masa duka suka kona shi kan batanci
- Babaji Sunday, kwamishinan yan sanda ya gargadi mutane kan daukan doka a hannunsu yana mai cewa an fara bincike kuma za a hukunta wadanda aka samu da laifi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta Abuja ta ce tana bincike kan kashe wani mutum da aka yi bisa zargin yin batanci a ranar Asabar a unguwar Lugbe a Abuja.
Hakan na zuwa ne a lokacin da rundunar ta gano sunan wanda aka kashe a matsayin Ahmad Usman wanda aka ce dan shekara 30 ne da haihuwa, rahoton The Punch.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta tabbatarwa The Punch hakan a ranar Asabar, ta kara da cewa rundunar ta fara bincike a kan lamarin.
Ta ce:
"Abubuwa sun koma yadda suke a unguwar yayin da jami'an mu suna cigaba da sa ido da tattara bayanai.
"Ana shawartar mazauna unguwar su cigaba da harkokinsu ba tare da tsoro ba a yayin da bincike ke gudana domin gano gaskiyar abin da ya yi sanadin afkuwar lamarin mara dadi da kuma kama masu hannu a ciki.
"Mun gano cewa wani Ahmad Usman mai shekaru 30 kuma dan vigilante ne a Tippa Garage a Gidajen Gwamnatin Tarayya da ke Lugbe a Abuja ya yi musayar maganganu da wani Mallami wanda kawo yanzu ba a gano sunansa ba.
"Musanyar maganganun da suka yi ta yi zafi har ta kai ga rikici ya barke aka kuma malamin ya tattaro mutane kimanin dari biyu suka kashe Ahmad Usman suka kona shi."
'Karar Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya
Yan sandan sun ce bayan samun rahoto, jami'ansu sun isa wurin sun kuma kwantar da tarzomar kafin ta wuce gona da iri.
Kwamishinan yan sanda na Abuja, Babaji Sunday, wanda ya yi magana da wakilin The Punch ya yu gargadin mutane su dena daukan doka a hannunsu.
Ya ce:
"Ba mu amince da daukan doka a hannu ba. Dokar Najeriya ya hana hakan kuma za a dauki mataki kan wadanda aka samu da hannu wurin aikata laifin."
Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja
Tunda farko, kun ji cewa wasu matasa a ranar Asabar sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW) a birnin tarayya Abuja.
Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit An tattaro cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe, rahoton Punch.
Wani mai idon shaida yace dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah amma yayi wani sabo da daren jiya.
Asali: Legit.ng