Yan sanda sun tarwatsa yan uwan fasinjojin jirgin kasa da aka sace yayin da suke zanga-zanga

Yan sanda sun tarwatsa yan uwan fasinjojin jirgin kasa da aka sace yayin da suke zanga-zanga

  • Zanga-zangar da yan uwan fasinjojin jirgin kasa da aka sace a hanyar Abuja-Kaduna suka shirya ya hadu da cikas
  • Yan sanda sun tsare masu zanga-zangar wadanda suka taru a Unity Fountain a hanyarsu ta zuwa majalisar dokokin tarayya sannan suka kora su
  • Jami'an tsaron sun yi ikirarin cewa yan uwan fasinjojin basu sanar da su cewa za su gudanar da tattakin ba

Abuja - Yan sanda a ranar Juma’a, 3 ga watan Yuni, sun tarwatsa wani zanga-zanga da yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka sace.

A ranar 28 ga watan Maris ne yan bindiga suka farmaki jirgin kasan Abuja-Kaduna, lamarin da ya kai ga mutuwar fasinjoji takwas yayin da aka sace wasu da dama.

Tuni dai yan uwan fasinjojin suke ta rokon gwamnatin tarayya a kan ta ceto masu masoyansu da ke tsare a hannun miyagun.

Kara karanta wannan

Gakuwa da mutane: 'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a babbar hanyar Kaduna

Yan sanda sun tarwatsa yan uwan fasinjojin jirgin kasa da aka sace yayin da suke zanga-zanga
Yan sanda sun tarwatsa yan uwan fasinjojin jirgin kasa da aka sace yayin da suke zanga-zanga Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yan uwan nasu sun taru a Unity Fountain dauke da kwaleyen sanarwa da rubutu kamar haka: “Wadanda aka sace suna rushewa a tsare”, “Ya shugaban kasa, dan Allah ka taimaka mana”, “Jininmu na kara hawa a kullun”, “Bama iya bacci da idanunmu a rufe” da dai sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun shirya yin tattaki zuwa majalisar dokokin tarayya amma sai yan sanda suka tsare su a hanya sannan suka kora su.

Yan sandan sun yi ikirarin cewa yan uwan fasinjojin basu sanar da su cewa za su yi zanga-zangar ba, rahoton Punch.

Da yake zantawa da manema labarai, daya daga cikin yan uwan fasinjan, Abdulmumin Mohammed, ya yi watsi da matakin yan sanda, yana mai cewa ya kamata su nuna tausayawa.

Ya nuna rashin gamsuwa da kokarin gwamnati na ceto wadanda aka sacen, inda ya bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan tabbatar da ‘yancinsu.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

Mohammed ya ce:

“Ya kamata jami’an yan sanda su nuna tausayawa. Kamata yayi ace sun shiga cikinmu a wannan fafutukar amma ba wai su aikata sabanin haka ba. Abun takaici ne. masoyanmu na tsare sama da kwanaki 60. Yawancinsu basa cikin yanayi mai kyau. Muna bukatar gwamnati ta gaggauta daukar mataki kan duk abun da suke yi. Wadanda abun ya ritsa da su suna mutuwa kuma bama jin dadin kanmu a gida.”

Kaduna: 'Yan sanda sun bindige 'yan bindiga 2 yayin dakile sabon farmakin da suka kai

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga su ka kai karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar.

Mohammed Jalige, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya saki ranar Alhamis, TheCable ta ruwaito.

Ya ce rundunar ta gano yadda su ka kai harin kauyen Kimdi da ke karamar hukumar Birnin Gwari ranar Talata, hakan ya sa su ka kai wa 'yan bindigan samame inda su ka halaka 'yan ta'adda biyu tare da kwace bindiga kirar AK 47.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng