Da Duminsa: Shugaba Buhari ya rattaɓa hannu a kasafin kudin 2022 da akai wa kwaskwarima
- Shugaba Buhari ya sa hannu kan kasafin kudi na shekarar 2022 bayan majalisar tarayya ta amince da shi a watan Disamba 2021
- Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai, Umar El-Yakub ya ce kasafin ya tsallake sharuɗɗan majalisa
- Bayanai sun nuna cewa ƙasafin ya kunshi kuɗaɗen da aka ware don biyan bashi da na harkokin yau da kullum da sauran su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rattaɓa hannun kan sabon kundin kasafin kudi 2022 da majalisun tarayya suka amince da shi ya zama doka, kamar yadda Channesl tv ta ruwaito.
Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai ta ƙasa, Umar I. El-Yakub, yace sabon ƙasafin ya tsallake sharuɗɗa majalisa ne a watan Disamba 2021.
Sabon kundin ya motsa daga asalin kasafin kuɗin tarayya zuwa Tiriliyan N17.319trn. An ware naira Biliyan N817.699trn na hakkokin ka'idojin tura kuɗi.
The Nation ta rahoto cewa kasafin ya ƙunshi kuɗi Tiriliyan N3.978trn da aka ware doon rage bashin da ake bin ƙasa, yayin da ak ware Tiriliyan ₦7.108trn na hatkokin yau da kullum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma kuɗin da aka ware tiriliyan ₦5.415trn domin ba da gudummuwa wajen cigaban kasa a shekarar wacce zata kare ranar 31 ga watan Disamba, 2022.
Atiku bai zaɓi abokin takara ba - Kakaki
A wani labarin na daban kuma Gaskiyar bayani kan wanda Atiku Abubakar ya zaɓa ya zama matamakinsa a zaɓen 2023
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar , bai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa ba har yanzun, a cewar hadiminsa, Mista Paul Ibe.
Mista Ibe ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa raɗe-raɗin da ke yawo a bakunan mutane da kafafen sada zumunta cewa Atiku ya zabi tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, ba gaskiya bane.
Asali: Legit.ng