Da Dumi-Dumi: Jirgin farko na mahajjatan bana zai tashi daga Najeriya mako mai zuwa

Da Dumi-Dumi: Jirgin farko na mahajjatan bana zai tashi daga Najeriya mako mai zuwa

  • Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ta ce a ranar 9 ga watan Yuni, jirgin farko zai kwashi alhazai zuwa Saudiyya
  • Shugaban hukumar na ƙasa, Zikirullah Hassan, ya ce sun amince da kamfanonin jirgaen sama uku da zasu yi aikin jigilar a bana
  • Ya ce NAHCON ta kammala duk wasu shirye-shirye kuma zuwa ranar Litinin zata tura tawaga Makkah za Madina

Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa insha Allahu jirgin farko da zai kwashi kashin farko na mahajjatan bana zar bar Najeriya zuwa Saudiyya mako mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto cewa hukumar ta sanar da cewa za'a fara jigilar mahajjatan bana 2022 daga Najeriya a ranar 9 ga watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Da yake jawabi yayin rattaɓa hannun kan yarjejeniya da kamfanonin da zasu aikin a Abuja ranar Jumu'a, shugaban NAHCON, Zikirullah Hassan, ya ce sun zaɓi ranar ne domin kammala duk wasu shirye-shirye.

Hukumar Alhazai.
Da Dumi-Dumi: Jirgin farko na mahajjatan bana zai tashi daga Najeriya mako mai zuwa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa sun zaɓi kamfanonin jiragen sama uku da zasu yi aikin jigilar Alhazan kuma sune; Azman Air, Max Air da kuma Flynas Airlines.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya roki kamfanonin jiragen uku da su yi aiki mai kyau ba tare da yin karan tsaye ga dokokin ma'aikatar sufurin jiragen sama ba kuma su mu'amalanci mahajja da kyau.

Zamu tura tawaga Makkah da Madina

Hassan ya kuma bayyana cewa a ranar 6 ga watan Yuni, tawagar hukumar NAHCON zasu nufi Makkah da Madina domin ƙarisa shirye-shirye a can.

NAN ta rahoto a kalamansa ya ce:

"Yau ta kasance rana mai dumbin tarihi saboda rana ce ta farko a ayyukan aikin hajjin bana 2022. Mun sani cewa idan babu jiragen sama mutanen da ke wajen Saudiyya ba zasu samu damar sauke farali ba."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola Tinubu

"Ku bani dama na taya kamfanonin jirgen da suka yi nasara murna, da su muke faɗi tashi a hukumar nan tun tale-tale. Haka nan muna fatan waɗan da ba'a zaɓa ba zasu yunkuro nan gaba."

A wani labarin kuma Gwamna ya faɗi wanda APC zata tsayar shugaban kasa idan har tana son cigaba da mulki a 2023

Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya shawarci APC ta tsayar da ɗan kudu ya gaji Buhari idan tana son cigaba da mulki a 2023.

Gwamnan, wanda aka ba shugaban kwamitin tsaro da haɗa kai na taron fidda gwani, ya ce sun cimma matsaya da sauran gwamnonin kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262