Kano: Gobara Ta Kashe Mahaifiya Da Ɗanta Mai Shekaru 3 a Gidansu
- Wata mummuan gobara da aka yi cikin daren ranar Alhamis a Gandun Albasa-Bala Burodo, Kano ta yi sanadin mutuwar wata da danta
- Saminu Abdullahi, Kakakin hukumar Kwana-Kwana na Jihar Kano ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a
- Abdullahi ya ce sun samu kiran neman dauki misalin karfe 2.07 na dare suka isa wurin 2.11 amma suka ciro mutanen biyu a sume, da aka kai su asibiti likitoci suka ce sun cika
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Wani abin bakin ciki ya faru a ranar Alhamis a unguwar Gandun Albasa-Bala Burodo, a Kano Municipality, a yayin da wata mahaifiyar yar shekara 35, Maryam Nura, da danta mai shekaru uku, suka mutu a gobarar da ta tashi a gidan da suke.
Hukumar kashe gobara na Jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, Saminu Abdullahi, a ranar Juma'a a Kano,rahoton NAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mr Abdullahi ya yi bayanin cewa gobarar ta faru ne a daren ranar Alhamis.
"Mun samu kiran neman dauki misalin karfe 2.07 na dare daga wani Ibrahim Ashiru kuma nan take muka tura tawagar mu zuwa wurin suka isa 2.11, " in ji shi.
Ya ce:
"gobarar ya cinye ginin, dakuna biyar mai kimanin tsawon kafa 7 da 7 baki dayansa."
Mr Abdullahi ya ce an ceto wadanda abin ya ritsa da su a sume aka kuma mika su ga Sufeta Shehu Lawal na caji ofis na Kwali, wanda ya garzaya da su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar sun rasu, Guardian ta rahoto.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng