Tinubu: Buhari dan Arewa ya dana mulki shekara 8, 2023 ta mu ce, mu Yarbawa

Tinubu: Buhari dan Arewa ya dana mulki shekara 8, 2023 ta mu ce, mu Yarbawa

  • Shugaban APC Tinubu ya bayyana cewa, yanzu lokaci ya yi da Yarbawa za su karbi mulkin Najeriya a zaben 2023
  • Ya bayyana haka ne yayin zantawa da deliget na jam'iyyar APC a jihar Ogun a jiya Alhamis kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Tinubu ya kuma bayyana cewa, shi ne kashin bayan siyasar Buhari da gwamna Abiodun na jihar Ogun

Jihar Ogun - Dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da Yarabawa za su kawo shugaban Najeriya na gaba a 2023.

Tinubu ya bayyana haka ne a dakin taro na masaukin shugaban kasa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget-deliget din APC gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar

Tinubu, wanda ya ce lokacin Yarbawa ne yanzu, ya kuma lura cewa lokaci ya yi da zai zama shugaban kasa, inji rahoton Punch.

Lokacin Yarbawa ne su mulki Najeriya a 2023
Tinubu: Buhari dan Arewa ya dana mulki shekara 8, 2023 ta mu ce, mu Yarbawa | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Jaridar Tribune Online ta naqalto jawabansa, Tinubu ya shaida cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A wannan karon, layin Yarbawa ne kuma a kasar Yarbawa, lokaci na ne."

Shugaban na APC na kasa ya samu rakiyar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a jihar Ogun; takwaransa na jihar Kano, Umar Ganduje, da tsohon gwamnan jihar Borno, Kasim Shettima.

A rahotonnin baya da suka gabata, Tinubu ya ce shi ya nada shugaba Buhari mulkin Najeriya, kuma shi ne kashin bayan siyasar Buhari a zaben 2015.

Hakazalika, ya kuma ce shi ya ba gwamnan jihar Ogun, Abiodun tikitin APC, kana ya daga hannunsu a zaben 2019, inda alamu ke nuna cikin fushi ya yi maganar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fito da abin da ya boye tun 2015, ya fadi yadda Buhari ya nemi suyi takara tare

Ya bayyana wadannan maganganu ne duba da yadda masana ke ganin Osinbajo Buhari zai zaba ba Tinubu domin gaje kujerarsa.

Ni na ba ka mulki: Tinubu ya caccaki gwamna ido-da-ido kan goyon bayan Osinbajo

A wani labarin, jaridar Punch ta ruwaito cewa, na gaba-gaba a tseren tikitin takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bol Tinubu ya yi ikrarin cewa ya daura gwamna Dapo Abionun na Ogun a shekara ta 2019.

Ya yi magana ne a masaukin shugabab kasa na Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin jawabi ga deliget-deliet na APC kafin zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC.

Tinubu na tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da takwaransa na jihar Kano, Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.