Abdulaziz Yari ya fito daga hannun EFCC, an fadi dalilin barin Akanta-Janar ya dawo gida

Abdulaziz Yari ya fito daga hannun EFCC, an fadi dalilin barin Akanta-Janar ya dawo gida

  • Sababbin bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa Alhaji Abdulaziz Yari ya bar hannun EFCC
  • ‘Yanuwan tsohon Gwamnan sun shaidawa manema labarai cewa ya dawo gida a ranar Alhamis
  • Hukumar EFCC ta ce ta ba Ahmed Idris beli, ana binciken Akanta Janar din ne da taba Baitul-mali

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta saki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

‘Yanuwa da dangin Alhaji Abdulaziz Yari ne suka shaidawa jaridar nan ta Daily Nigerian wannan labarin a yau, ranar Juma’a, 6 ga watan Maris 2022.

Kamar yadda na-kusa da tsohon gwamnan suka tabbatarwa manema labarai, an saki Yari ne a jiya.

Idan za a tuna, jami’an EFCC sun yi ram da tsohon gwamnan na Zamfara a gidansa a unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja a makon nan.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ganduje ya haramta amfani da Adaidaita sahu da daddare a Kano

Kashin da ke jikin Yari

Ana zargin akwai hannun Yari a badakalar da ake tuhumar Ahmed Idris da tafkawa na akalla Naira biliyan 84 a lokacin da yake kujerar Akanta Janar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta ce an kama ‘dan siyasar ne tare da babban darektan kamfanin Finex Professional.

Abdulaziz Yari
Jigon APC, Abdulaziz Yari Hoto: Najeeb Al Zamfarawy
Asali: Facebook

Idan zargin da ake yi ya tabbata, Yari ya amfana da Naira biliyan 22 daga cikin Naira biliyan 84 da ake tunani AGF din ya karkatar daga baitul-mali.

Zargin shi ne Yari wanda shi jam’iyyar APC ta ba takarar kujerar Sanatan yammacin Zamfara ya amfana da kudin ta kamfanin Finex Professional.

Ahmed Idris ya samu beli

A gefe guda, Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da cewa an saki Babban Akawun din gwamnatin tarayya.

Vanguard ta rahoto Wilson Uwujaren yana cewa an bada belin Ahmad Idris ne a yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Karin hasken da kakakin EFCC ya yi, ya nuna ba an kyale Idris ba ne, ya samu ‘yanci ne domin ya yi belin kan shi kamar dai yadda doka tayi tanadi.

Shari'ar Abduljabbar Kabara

A wata Duniyar, an ji labari, Shehin malamin nan, Abduljabbar Nasiru Kabara ya bukaci a ba shi lauyan da zai kare shi, ba tare da ya biya ko sisi ba.

An hana Sheikh Abduljabbar Kabara lauyan saboda yana iya samun kudin da ya haura N30, 0000. Wannan kudi shi ne mafi karancin albashi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng