Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015
- Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana yadda ya taimakawa wajen kawo shugaba Buhari mulki a zaben 2015
- A cewarsa, ba dan shi ba da shugaban bai samu damar mulkar Najeriya ba, haka nan ga mataimakin shugaban kasa Osinbajo
- Ya shaida cewa, shi ne jigon da ya taka rawar gani domin ganin jam'iyyar ta samu karbuwa kana ta yi mulki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kai ga hayewar shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015.
Tinubu ya kuma ce shi ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi magana ne a dakin taro namasaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget din jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Tinubu a lokacin yana tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da takwaransa na Kano, Umar Ganduje, da kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kasim Shettima, inji rahoton TheCable.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ni na kawo Osinbajo matsayin da yake
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce ya bayyana hakan ne a karon farko a jihar Ogun, mahaifar Osinbajo, daya daga cikin abokan gogawarsa a takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Ya ce Buhari ya ba shi tikitin tsayawa takara tare dashi, amma wasu batutuwa suka taso, lamarin da ya haifar da kawo batun tikitin takarar musulmi da musulmi a 2015.
Tsohon gwamnan ya kuma ce a lokacin da aka neme shi da ya mika sunayen wadanda za su tsaya takara har guda uku, ya ba da sunayen Yemi Kadoso, Wale Edun da Yemi Osinbajo.
Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu
Ya kara da cewa daga baya aka tsayar da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari.
Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya ce burinsa na siyasa ya fi kasuwa a Arewacin Najeriya fiye da kowane yankunan kasar nan, inji rahoton Daily Trust.
Okorocha ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan batutuwan da suka shafi zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki.
Okorocha dai na fuskantar tuhume-tuhume 17 bisa zargin karkatar da kudade daga asusun hadin gwiwa na gidan gwamnatin Imo da na kananan hukumomi zuwa wasu kamfanoni masu zaman kansu tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.
Asali: Legit.ng