Yanzu mu ma za mu fara kare kan mu da kan mu - Majalisar dattawan Arewa

Yanzu mu ma za mu fara kare kan mu da kan mu - Majalisar dattawan Arewa

Mataimakin sakatarenmajalisar dattawan al'ummar kabilar Yarbawa mai suna Alhaji Suleiman Salami ya baiwa 'yan Najeriya musamman yan kabilar sa da cewa kar su sake su bar tsaron dukkan rayuwar su ga jami'an tsaron kasar.

Alhaji Suleiman Salami mai shekaru 81 a duniya din dai yayi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da yayi da majiyar mu ta wayar tarho a garin Osogbo a ranar Lahadin da ta gabata.

Yanzu mu ma za mu fara kare kan mu da kan mu - Majalisar dattawan Arewa
Yanzu mu ma za mu fara kare kan mu da kan mu - Majalisar dattawan Arewa

KU KARANTA: Ko kun san wacece tsohuwar matar Dangote, Hajiya Zainab?

Legit.ng ta samu cewa ya kuma kara da cewa tabbas ya amince da dukkan kalaman da tsohon jami'in rundunar sojin Najeriya kuma tsohon ministan tsaron kasar watau TY Danjuma yayi inda ya shawarci mutanen kabilar sa da su dauki matakin kare kan su tun da jami'an tsaron sun kasa.

A wani labarin kuma, Yanzu haka ana cikin zaman dar dar a tsakanin manyan shugabannin hukumar rundunar 'yan sandan Najeriya bayan da wani bincike na hukumar harkokin kudi ya bankado akalla jami'an 'yan sanda dubu 78 da dari 315 na bogi da kuma gwamnati ke biya albashi duk wata.

Haka zalika ma dai ma'aikatar kudin ta gwamnatin tarayyar ta kuma bayyana cewa ta samu nasarar yin tsime na akalla Naira biliyan 68 na kudaden gudanarwa a cikin shekarar ta 2017.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng