Zamfara: Dumu-dumu an kama magidanci da sassan jikin mutum

Zamfara: Dumu-dumu an kama magidanci da sassan jikin mutum

  • 'Yan sandan jihar Zamfara sun yi ram da wani da ake zarginsa da kisan kai, Jabiru Ibrahim daga gundumar Dauran ta karamar hukumar Zurmi da hannun mutum
  • Sai dai, bincike ya bayyana yadda wanda ake zargin yake cikin wata kungiyar ta'addancin 'yan sa kai wadanda ke cin karensu ba babbaka tare da daukar doka a hannunsu a yankin
  • Haka zalika, wanda ake zargin ya bayyana yadda shi da wasu abokan harkallarsa 3 suka wa wani Abdullah, bafulatani kisan gilla daga bisani ya datse hannun daman mamacin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - 'Yan sandan jihar Zamfara sun yi ram da wani da ake zargin 'dan sa kai ne bayan an kama shi da sassan jikin mutum, Channels TV ta ruwaito.

A wata takarda da rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta fitar a ranar Litinin ta bayyana yadda ake zargin Jabiru Ibrahim daga gundumar Dauran a cikin karamar hukumar Zurmi ta jihar.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 7, an fara kama wadanda ake zargi da fille kan ‘Dan Majalisa a Anambra

Zamfara: Dumu-dumu an kama magidanci da sassan jikin mutum
Zamfara: Dumu-dumu an kama magidanci da sassan jikin mutum. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Hadin guiwar 'yan sanda da jami'an tsaron da ke yaki da ta'addanci tsakanin Dauran zuwa Zurmi sun yi ram da wanda ake zargin gami da mika shi hedkwatar rundunar 'yan sandan da ke Gusau don cigaba da bincikarsa,"

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, Muhammad Shehu ya bayyana a takardar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A iya binciken da aka gabatar, ya bayyana yadda wanda ake zargin yake cikin kungiyar 'yan sa kai wadanda suka dauki tsawon lokaci suna cin karensu ba babbaka a yankin Dauran tare da daukar doka a hannunsu, wanda ke janyo 'yan bindiga yawan kai hare-haren daukar fansa ga mutanen yankin ba su ji ba ba su gani ba.
"Yayin da aka kama wanda ake zargin, ya bayyana yadda shi da wasu uku daga cikin 'yan kungiyarsu suka yi wa wani Abdullah, bafulatani kisan gilla, daga bisani wanda ake zargin ya yanke hannun daman mamacin."

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

Har ila yau, ana cigaba da bincike don cafko sauran abokan harkallarsa tare da yi wa lamarin garanbawul kafin a gurfanar da su gaban kotu, a cewarsa.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

A wani labari na daban, mutane bakwai ne suka halaka yayin da wasu uku suka jigata a ranar Talata, 24 ga watan Mayu yayin wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Miyagun wadanda aka kintata yawansu ya kai 150, sun bayyana wurin karfe 6 na yammaci, HumAngle ta ruwaito.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Alhaji Maidawa mai shekaru 53 mazaunin Tungar-Wakaso, ya samu harbin bindiga a bayansa, kwauri da kafadarsa yayin farmakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel