Rikici: Tsagerun IPOB sun mamaye makarantu, sun fatattaki dalibai saboda wani dalili
- An samu tashin hankali a jihar Anambra yayin da 'yan IPOB ke kokarin kakaba dokar zaman gida saboda tunawa da ranar Biafra
- Wannan na zuwa ne baya ga dokar da suka kakabawa mutanen jihar kan kowace ranar Litinin, inda suke hana fita
- Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, tsagerun sun kuma yi arangama da jami'an tsaro, duk da ma ba a tabbatar ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Anambra - An samu tashin hankali yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan IPOB ne suka mamaye makarantu a garin Onitsha da wasu sassan yankin Idemili na jihar Anambra inda suka fatattaki dalibai daga ajujuwa.
An ce ‘yan bindigar sun kuma mamaye kasuwanni da wuraren taruwar jama’a domin fatattakar mutane.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun umarci mutane da su koma gida suna masu cewa yau ne “Ranar Biafra”.
Ana ware kowace ranar 30 ga watan Mayu duk shekara domin bikin ranar Biafra amma a bana an samu tasgaro kasancewar ranar ta zo daidai da ranar Litinin da tsagerun IPOB ke kakaba dokar zaman gida kan jama'ar yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ce tsagerun sun dage cewa dole ne a yi zaman gida domin yin bikin ranar Biafra na shekara domin jiya Litinin ce ta zaman gida ba ranar Biafra ba.
Tuni dai aka fara fargabar ko za a fita ko a’a, kuma wasu daga cikin mutanen da suka fito suka fara komawa gidajensu, inji jaridar Punch.
An kuma tattaro cewa an yi ta harbe-harbe tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar a yankin Idemili, haka nan Pulse ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, bai amsa kiran da aka yi masa don tabbatar da faruwar lamarin ba.
Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni
A wani labarin, Shugaban Cocin Methodist, Samuel Uche, a ranar Talata ya ce an biya Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin 'yan bindiga su sake shi, Channels Tv ruwaito.
A wani taron manema labarai a Legas, malamin ya ce an shirya kudaden ne a buhu biyar na Naira miliyan 20 kowanne, kuma Cocin Methodist a Najeriya ne ya tara kudaden.
Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ko ta jiha, ko sojoji ko ‘yan sanda ba su shiga tsakani ba a lamarin.
Asali: Legit.ng