EFCC ta ayyana neman wani tsohon ɗan majalisa ruwa a jallo kan tsallake beli
- Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon ɗan majalisar tarayya ruwa a jallo bisa wasu dalilai guda biyu
- A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, EFCC ta ce Mista Nzeribe, ya tsallake sharuddan beli da kotu ta ba shi kuma ya daina halartar shari'a
- Hukumar ta gurfanar da tsohon ɗan majalisar kan tuhuma hudu, kuma Kotun tarayya ta kama shi da laifukan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa (EFCC) ta ayyana neman tsohon mamba a majalisar wakilan tarayya, Marcellinus Nzeribe, bisa tsallake sharuddan beli da guje wa shari'a.
Hukumar ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta saki ranar Litinin a shafinta na dandalin sada zumunta Facebook.
Bayanai sun nuna cewa ranar Litinin ta makon da ya gabata, Babbar Kotun tarayya da ke zama a Abuja ta kama Mista Nzeribe da laifi kan tuhume-tuhume hudu.
Mai Shari'a Halilu Yusuf, ya kama tsohon ɗan majalisar da laifin aikata sojan gona, mallakar wasu takardun FG da kuma amfani da su wajen damfarar filaye a Anguwar Maitama Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa EFCC ke nemansa ruwa a jallo?
A sanarwan neman tsohon ɗan majalisar, EFCC ta ce Nzeribe ya tsallake sharuɗɗan belin da Kotu ta ba shi kuma ya ɓata ba'a sake ganinsa ba tun wancan lokacin.
EFCC ta ce:
"Muna sanar da al'umma cewa hukumar EFCC na neman Marcellinus Chkwumaze Nzeribe ruwa a jallo a Kes ɗin amfani da takardun bogi."
"Adireshi na ƙarshe da aka san ya zauna a wurin kafin bacewarsa shi ne Block M7, Flat 8, a jerin gidaje NNPC da ke Area 11, a Garki, birnin tarayya Abuja."
Bugu da kari hukumar yaƙi da masu rashawa ta roki yan Najeriya su talllafa mata da bayanan sirri, waɗan da sa zasu sauƙaƙa wa jami'ai wajen cafke tsohon ɗan majalisar.
"Duk wanda ke da bayanan sirri kan inda ya ɓuya, Dan Allah ya tuntuɓi ofishin EFCC ma fi kusa ko kuma ya kai rahoto Caji Ofis na yan sanda da sauran hukumomin tsaro."
A wani labarin na daban kuma Wani Magidanci ya halaka wani mutumi kan kuɗin gutsuren Burodi N100
Kotu ta umarci a cigaba da tsare wani mutumi, Alhaji Haruna Adu, bisa zargin kashe wani mai Burodi kan kudi N100 a Kwara.
Jami'in hukumar yan sanda mai gabatar da ƙara, Innocent Owoola, ya shaidawa Kotun Majirtire da ke zamanta Ilorin duk abin da ya faru.
Asali: Legit.ng