Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Malaman Makarantun Poly Godiya Saboda Komawa Bakin Aiki
- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yaba wa kungiyar malaman Kwalejin Fasaha, ASUP, kan janye yajin aikin gargadi da ta shiga a baya-bayan nan
- Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka ne ya yi wannan godiyar cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatarsa, Olajide Oshundun ya fitar a madadinsa
- Ngige ya ce wannan shine abin da ya dace kuma ya shawarci kungiyoyin makarantu da ke yajin aiki su yi koyi da ASUP su janye yajin aikin yayin da gwamnati ke cigaba da warware musu matsalolin da ke damunsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi wa Kungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha, ASUP, godiya saboda janye yajin aikin gargadi tare da koma wa bakin aiki, rahoton Vanguard.
Gwamnatin ta kuma jinjina wa kungiyar saboda duba kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi domin warware matsalolin da ke fuskantar ilimin kwalejojin fasaha a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Kwadago da Samar Da Aikin Yi, Chris Ngige cikin wata sanarwa da Shugaban Sashin Hulda da Al'umma na Ma'aikatar Kwadago da Ayyuka, Olajide Oshundun ya fitar a madadinsa ya ce abin farin ciki ne cewa malaman sun yi na'am da kokarin da gwamnati ke yi don inganta ilimi a kasar.
An rahoto ministan na cewa, "ASUP ta yi gagarumin abin a yaba mata a lokacin da wasu kungiyoyin da ke yajin aiki ba su amincewa gwamnati ta motsa ko da allura ne domin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma yayin sulhu.
"Ba nan kawai kungiyar ta tsaya ba, ta kuma lissafo wasu cikin bukatun da gwamnati ta biya musu, yayin da suke fatan za a cika musu sauran."
FG ta shawarci sauran kungiyoyin malamai su yi koyi da ASUP
"Wannan shine hanyar da ya dace a rika bi, abin da ya kamata sauran kungiyoyi a bangaren ilimi su kwaikwaya, domin cigaba don warware kallubalen da ke shafar bangaren ilimin manyan makarantu."
Ya bada tabbacin cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin cika musu sauran alkawurran, Sun News ta rahoto.
A sanarwar da ASUP ta fitar na janye yajin aikin, ta ce tana fatan za a cika mata sauran alkawurran kafin kwamitin NEC dinta su yi taro a ranar 22 ga watan Yunin 2022.
Martanin wasu dalibai game da janye yajin aikin na ASUP
Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu dalibai domin jin martaninsu game da janye yajin aikin da ASUP ta yi.
Galibin daliban sun nuna farin cikinsu game da janye yajin aikin suna kuma fatan ba za a sake komawa ba nan gaba. Sannan suna fatan ganin sauye-sauye a makarantunsu da zai inganta karatunsu.
Aminu Mohammad, dalibi dan aji biyu na Poly ta Jihar Jigawa ya ce:
"Na yi matukar farin cikin samun labarin janye yajin aikin, babu dadi zaman gida babu karatu tare da bata lokaci yayin da abokanmu na makarantun kudi suke cigaba da karatu."
Musa Kabir shi kuma cewa ya yi:
"Gaskiya na ji dadi sosai, zaman gidan duk da ba mu dade irin na daliban jami'a ba tuni ya ginshe ni."
Wasu daliban da dama da suka nemi a sakayya sunansu suma sun ce dama sun kosa a daidaita domin zaman hakan nan da suke yi ba alheri bane gare su kuma iyayensu dama ba su jin dadi.
Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu
A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.
Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.
Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.
Asali: Legit.ng