Nan da 2026, Gaba daya kudin shigan Najeriya bashi za'a rika biya da su: Asusun Lamunin Duniya

Nan da 2026, Gaba daya kudin shigan Najeriya bashi za'a rika biya da su: Asusun Lamunin Duniya

  • Da yiwuwan gwamnati ta gaza biyan kudin ma'aikata saboda yawan bashin da yayi mata katutu
  • Asusun lamunin duniya ya ce idan ba'a dau mataki ba nan gaba dukka kudin shigar Najeriya bashi za'a biya da su
  • Asusun ya yi takaicin yadda Najeriya ke cikin wannan hali duk da arzikin man feturin da take da shi

Abuja - Asusun lamunin duniya watau The International Monetary Fund (IMF) ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya bashi zata rika biya da kudin shiganta gaba daya.

Wakilin IMF dake Najeriya, Ari Aisen, ya bayyana hakan ranar Litnin yayin gabatar da bayanan tattalin arzikin yankin Sahara a birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Ya ce yanzu haka kashi 89% na kudin shigan Najeriya basussuka ake biya da su.

Kara karanta wannan

Romon Damokaradiyya: Jerin Ayyuka 20 da Garin Daura ya Mora Daga Mulkin Buhari

Yace:

"Babban abin lura game da Najeriya shine kudin ruwan da ake biya na basussuka daga kudin shiga na da yawa. Ana kiyasin cewa nan da 2026, dukkan kudin shiga basussuka za'a biya da su."
"Yanzu kashi 89% bashi ake biya da su kuma idan ba'a dau mataki ba, tashi zai kara yi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan na nuni ga rashin isasshen kudin shiga wa kasar. Kasar na bukatan fadada hanyoyin samun kudin shiga don tayi karfi."

Asusun Lamunin Duniya
Nan da 2026, Gaba daya kudin shigan Najeriya bashi za'a rika biya da su: Asusun Lamunin Duniya Hoto: imf.org

IMF ya kara da cewa kawo karshen shekarar nan ta 2022, kudin tallafin mai da gwamnati za ta rika biya zai iya kaiwa N6 trillion.

Tsakanin Junairu da Afrilu 2022, Najeriya ta biya N947.53 billion matsayin tallafin kudin mai.

Ari Aisen yace abin takaici shine Najeriya mai dimbin arzkin mai ta gaza amfani da daman tashi farashin danyen mai wajen gina asusun kudinta.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

Amma ya ce yana kyautata zaton cewa matatar man Dangote zai taimaka wajen rage fitar da mai da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel