Romon Damokaradiyya: Jerin Ayyuka 20 da Garin Daura ya Mora Daga Mulkin Buhari

Romon Damokaradiyya: Jerin Ayyuka 20 da Garin Daura ya Mora Daga Mulkin Buhari

Mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta Daura dake jihar Katsina ta fuskanci bayyanannen canji tun lokacin da shugaban kasar ya dare mafadun iko a shekarar 2015.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An ruwaito yadda birnin ya rikida ya koma birnin kasuwanci wanda ya tumbatsa da tarin kwangiloli daga gwamnatin tarayya da na jiha duk da masana'antun da ba na gwamnati ba.

Romon Damokaradiyya: Jerin Ayyuka 21 da Garin Daura ya Mora Daga Mulkin Buhari
Romon Damokaradiyya: Jerin Ayyuka 21 da Garin Daura ya Mora Daga Mulkin Buhari. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Sauya fasalin da birnin ya yi ya fara ne jim kadan bayan darewar Buhari madafun iko a shekarar 2015 wanda ya rikide daga kauye mara cinkoso da hayaniya, wadanda manyan sana'oin mazauna yankin su ne noma, kananan sana'oi da kiwon dabbobi zuwa wani irin gawurtaccen gari cike da manyan sana'oi a jihar Katsina.

Jaridar Punch ta ruwaito yadda a halin yanzu fasalin gine-ginen Daura ya tumbatsa zuwa gine-ginen zamani masu kayatarwa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Bugu da kari har da titi da hanyoyin ruwa masu kyau wanda ya kara kayata birnin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga irin cigaban da birnin ya samu

1. Asibitin hafsin sojin saman Najeriya, Asibitin Gaggawa na hafsin sojin saman Najeriya na tarayya.

2. Jami'ar Tarayya ta sufuri.

3. Filin wasannin Birnin Daura

4. Bataliyan Sojin kasan Najeriya na 171.

5. Foliteknik na Tarayya dake Daura

6. Asibitin mata da kananan yara

7. Aikin tagwayen titin Kano zuwa Kongolam wanda aka tsara zairatsa ta Daura da Makarantar mutane masu bukata ta musamman a Daura.

8. Sashen martanin gaggawa na Sojin saman Najeriya, Daura.

9. Sansanin bataliya ta 171 ta sojn kasan Najeriya, Daura.

10. Sansanin aiki na sojin kasa na Najeriya kan titin Kongolam, Daura.

11. Cibiyar samar da aikin yi ta kasa, Ganga, Daura

12. Gyara da fadada karamin filin wasa na Daura.

Kara karanta wannan

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

13. Cibiyar koyar da sana'o'in dogaro da kai, titin Zango, Daura.

14. Kammala Sabke Dam, Daura, wanda ke samar da lita miliyan daya na ruwa ga Daura da al'umma masu makwabtaka.

15. 132KVA layin wutar lantarki daga Katsina zuwa Daura da tiransifomomi masu karfin 30 da 40 MVA domin inganta wutar lantarki.

16. Dakin mata mai gado 50 a babban asibitin Daura.

17. Dakin karatu na yanar gizo na Sir Emeka Offor, Daura.

18. Gyara, fadada, farfadowa da kammala ayyuka da yawa da aka yi watsi da su kamar tituna, makarantu, magudanun ruwa da sauransu.

19. Tsarin ruwa mai amfani da hasken rana da ke samar da lita 400,000 wanda NNPC da Belema Ol tare da hadin kan gidauniyar Jack-Rich Tein suka samar.

20. Cibiyar koyar da kwalliya da raba kayayyakin kwallaiya ga mata 1000 a Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel