Borno: Jami'an MNJTF sun bindige 'yan ta'addan ISWAP 25, sun yi rashin jami'i 1
- Jami'an tsaron MNJTF tare da na Operation Hadin Kai sun kai samame ga 'yan ta'adda a Tumbun Rago, Tumbun Dilla da alkaryar Jamina cikin tsibirin tafkin Cadi
- A samamen da suka kai, sun yi nasarar sheke a kalla 'yan ta'adda 25 tare da gano bindiga kirar AK-47 1, bindigar harbo jirgin sama 1, daruruwan carbin harsasai, motar bindiga 1
- Hakan na nuna irin nasarorin da hukumar tsaron hadin guiwar kasashe ke cigaba da samu a Operation Lake Sanity da take aiwatar wa tafkin Cadi
Borno - Jami'an tsaron hadin guiwa ta kasashe (MNJTF) yayin kokarin ganin karshen ta'addanci a yankin tafkin Chadi, ta na cigaba da samun nasarori kan ayyukan yaki da ta'addanci.
PRNigeria ta ruwaito cewa, dakarun jami'an tsaron hadin guiwar kasashe tare da na Operation Hadin Kai sun kai samame cikin yankin Tumbun Rago, Tumbun Dilla da alkaryar Jamina a tsakiyar tsibirin tafkin Cadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dakarun tare da luguden wutar MNJTF / Operation Hadin kai sun jagoranci sheke sama da 'yan ta'adda 25 gami da gano bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigar harbo jirgin sama daya, da daruruwan carbin harsasai.
Haka zalika, an gano motar bindiga dake da tambarin Kamaru Gendarme dauke da makamai, wacce aka kama tare da tarwatsa ta, kayayyakin gida da suka hada da kayan makaranta da baburan 11 na ISWAP wadanda aka kama tare da kana wa, yayin da aka gano injinan ban ruwa biyu tare da kona gaba daya a sansanin.
Yayin kokarinsu na ranta a na kare, hatsabiban sun bar 'dansu mai shekaru 5 mai suna Babagana, za a mika yaron wanda ke cikin koshin lafiya ga hukumomin da suka dace.
Kala-Balge: Hadimin Zulum ya tabbatar da salwantar rayuka 32, yace ba manoma bane
A wani labari na daban, mutum talatin da biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da Boko Haram/ ISWAP suka kai wurin kauyen Mudu, kilomita 45 daga Rann, hedkwatar Kala-Balge a jihar Borno a ranakun karshen mako da suka gabata.
Mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da yawan wadanda aka halaka a bayanin da ya sakar wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri.
Vanguard ta ruwaito cewa, takardar da aka fitar ta tabbatar da ca mutum shida sun jigata yayin da wasu biyu suka tsallake farmakin da kyar.
Asali: Legit.ng