Kala-Balge: Hadimin Zulum ya tabbatar da salwantar rayuka 32, yace ba manoma bane

Kala-Balge: Hadimin Zulum ya tabbatar da salwantar rayuka 32, yace ba manoma bane

  • Hadimin Zulum, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da salwantar rayukan matasa 32 a kauyen Mudu da ke karamar hukumar Kala-Balge
  • Gusau ya tabbatar da cewa matasan ba manoma bane, masu neman karafuna ne suna siyarwa wadanda Boko Haram suka ritsa su a kauyen Mudu
  • Ya ce sojoji sun tarar da gawawwakinsu a daure yayin da wasu mutum shida suka jigata, sai mutum biyu da suka sha da kyar

Borno - Mutum talatin da biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da Boko Haram/ ISWAP suka kai wurin kauyen Mudu, kilomita 45 daga Rann, hedkwatar Kala-Balge a jihar Borno a ranakun karshen mako da suka gabata.

Mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da yawan wadanda aka halaka a bayanin da ya sakar wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

Kala-Balge: Hadimin Zulum ya tabbatar da salwantar rayuka 32, yace ba manoma bane
Kala-Balge: Hadimin Zulum ya tabbatar da salwantar rayuka 32, yace ba manoma bane. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, takardar da aka fitar ta tabbatar da ca mutum shida sun jigata yayin da wasu biyu suka tsallake farmakin da kyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamna Babagana Umara Zulum ya matukar damuwa da kisan jama'a a cikin ranakun karshen makon nan.
"Kafin fitar cikakken rahoto, gwamnan ya samu bayani daga shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Borno, Mohammed Dige, wanda ke wakiltar kala-Balge inda wadanda lamarin ya ritsa dasu," Gusau ya ce.
"Daga bayanin dan majalisar, an halaka matasa 32. Matasan ba manoma bane amma matasa ne masu dogaro da kansu da ke sana'ar karfe wanda ake kira da Kyadi.
"Wadanda lamarin ya ritsa da su sun je kauyen Mudu ne da ke karamar hukumar Dikwa ta jihar wanda ke da nisan kilomita 45 daga Rann a Kala-Balge suna neman karafuna. Amma a hakan suka ci karo da mummunan lamarin inda 'yan ta'addan suka yi musu kwanton bauna. mutum shida sun samu rauni yayin da biyu suka tsere," ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

"Tawagar sojoji tare da shugaban karamar hukumar Kala-Balge a ranar Talata sun samo gawawwaki 14 wadanda aka daure su sannan aka harbe su", kakakin Zulum yace.
"Gwamna Zulum ya matukar jajanta wa iyalan wadanda aka halaka da jama'ar Kala-Balge kuma yana jiran rahoton lamarin kafin ya dauka matakan da suka dace," Gusau yace.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

A wani labari na daban, mutane bakwai ne suka halaka yayin da wasu uku suka jigata a ranar Talata, 24 ga watan Mayu yayin wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Miyagun wadanda aka kintata yawansu ya kai 150, sun bayyana wurin karfe 6 na yammaci, HumAngle ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel