Ni ne nan namijin duniya: Wani bakin fata ya saki hotunan yara 33 da ya haifa da yan mata daban-daban
- Mutane sun caccaki wani mutumi mai suna Demond George, bayan ya nuna yara 33 da ya haifa da yan mata daban-daban
- Mutumin ya bayyana kansa a matsayin namijin duniya a wata wallafa da ya yi a shafin Facebook, yana mai cewa ba za a taba mantawa da tarihin da ya kafa ba
- Uba ga yaran 33 wanda bai nuna nadamar abun da ya aikata ba ya yi martani ga masu sukarsa a wani sabon bidiyo
Wani bakin fata da aka ambata da suna Demond George ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya nuna yara 33 da ya haifa.
A wata wallafa da ya yi a shafin Facebook a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, Desmond ya nuna hotunan yaransa sanye da tufafi mai launin baki iri daya dauke da rubutun ‘The LEGACY’ rubuce a gaba.
Legit.ng ta samu labarin cewa Demond ya haifi yaran ne tare da yan matansa daban-daban.
A wallafar tasa, Demond ya ce ‘wannan gadon zai ci gaba har abada’ yayin da ya bayyana sunayen wasu mutane da suka saka wannan daukar hoto nasu ya tabbata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai ya bayyana cewa tara daga cikin yaran basa cikin hoton.
Wallafar tasa ta shahara sannan mutane da dama sun caccake shi.
Da yake martani ga masu sukarsa a sabon bidiyo, Demond ya caccake su shima cewa shi ba ragwan namiji bane.
Ya ce:
“Ni ba rago bane. Kawai dai bana janyewa ne. Bana janyewa.”
Jama’a sun caccake shi
Cabbage Patch ya ce:
“Kyakkyawan iyali na jinjina maka. Kana iya kara 30+. Ka ci gaba da nuna masu da basu soyayya, lokaci sannan ka ci gaba da karfin aljihu Allah ya albarkace ka Demond George ni uwa ce ga yara 7!! Yara ni’ima ne.”
Zaɓen Fidda Gwani: An Kashe Mutum 2 Yayin Rikicin Da Ya Ɓarke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaɓen APC a Legas
Carrie Gareave ya ce:
“Ya kamata gwamnati su karbe kudinsu. Da gangan ya rusa gidaje, inda ya haddasawa gwamnati daukar nauyin yaransa. Hakan ba daidai bane a matakai da dama. Kuma kakar ta ji kunya da ta kasance cikin wannan rashin hankalin.”
Shayla Victoria ta ce:
"Wannan mummunan lamari ne kuma abin kunya. Wannan ba shine ma'anar gado ba. Wannan kunci ne. Wadannan kananan yaran da basu san komai ba. Karfin zuciya da tunani da ‘da daya ke bukata. Akwai laifin iyaye matan. Da alama bai auri ko daya daga cikinsu ba. Abun kyama.”
Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata
A wani labarin, wani matashi da ya gaji da duniya har yake ji kamar kada ya farka daga bacci saboda damuwa ya samu taimako.
Mutumin na da burin ganin ya mallaki mota nasa na kansa amma bai cimma wannan kudiri ba.
A wata rana, yace yana ta tunanin kashe kansa saboda yana fama da matsala ta damuwa. Amma a kan hanyarsa sai ya hadu da wata matashiyar mata sannan ta taimaka wajen cika masa daya daga cikin burikansa na siyan mota wanda kudinsa ya kai naira dubu 415.
Asali: Legit.ng