EFCC: Babban dalilin da ya sa muka kwamushe tsohon gwamnan Zamfara

EFCC: Babban dalilin da ya sa muka kwamushe tsohon gwamnan Zamfara

  • Hukumar EFCC ta magantu bayan kame gwamnan jihar Zamfara kan zargin rashawa da karkatar da kudade
  • EFCC ta ce ta gano yadda Yari ya karbi wani kaso daga kudaden da Akanta Janar Ahmed Idris ya wawashe daga baitul-mali
  • Wannan kame dai na zuwa ne bayan da hukumar ta fara tatsar bayanai daga Akanta Janar din da aka kame

Hukumar EFCC, ta yi bayani kan dalilin da yasa ta kame tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Hukumar ta ce ta kama Yari ne bisa zarginsa da hannu a badakalar Naira biliyan 84 da ake zargin tsohon Akanta Janar na Tarayya, AGF, Ahmed Idris dashi.

Wata majiya mai karfi a hukumar ta EFCC ta bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170

EFCC: Babban dalilin da ya sa muka kwamushe tsohon gwamnan Zamfara
EFCC: Babban dalilin da ya sa muka kwamushe tsohon gwamnan Zamfara | Hoto: ripplenigeria.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce an kuma kama shugaba kuma Manajan Darakta na Finex Professional, Anthony Yaro tare da tsohon gwamnan, inji Daily Nigerian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an kama mutanen biyu ne a ranar Lahadi bisa zarginsu da hannu a zarge-zargen cin kudin kasa.

A cewar majiyar, Yari wanda aka dauko shi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi, ya ci Naira biliyan 22 ta hannun Finex Professional.

Majiyar ta ce tsohon AGF ya baiwa wani Akindele kudin ne daga Naira biliyan 84 ta hannun Finex Professional.

Yadda aka kama AGF bisa zargin rashawa

Idan ba a manta ba an kama tsohon AGF ne a ranar 16 ga watan Mayu bisa zargin karkatar da kudin da suka kai Naira biliyan 84, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wasu rahotanni sun nuna cewa Idris, da ake zargin ya wawure kudaden ne ta hanyar amfani da aikin kwararrun bogi da kuma wasu ayyukan da suka sabawa doka ta hanyar amfani da ‘yan uwansa da makusantansa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Rahotanni sun ce an karkatar da kudaden ne ta hanyar zuba jarin gidaje a Kano da Abuja.

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A wani labarin, bincike kan makuden kudaden da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, game da dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, ya haura ya kai N170 biliyan, rahoton jaridar The Nation ya bayyana.

Idris, wanda a daren jiya ya ke neman a bada belinsa, ya bayyana sunayen wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu cikin handamar kudaden kasar da ake tuhumarsa a kai.

Hukumar EFCC ta tuhumi wani babban sakataren gwamnati kan wasu daga cikin kudaden da ake zarginsa da rub da ciki a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.