Dan'uwan Buhari, da wasu yan majalisar Katsina 6 da suka sha kashi a zaben fidda gwani

Dan'uwan Buhari, da wasu yan majalisar Katsina 6 da suka sha kashi a zaben fidda gwani

Yan majalisar wakilan tarayya guda takwas sun sha kashi a zaben fidda gwanin yan majalisa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ya gudana ranar Juma'a.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wadannan yan majalisa duk da su ke kan mulki sun sha lallasa hannun abokan hamayyarsu a zaben fidda gwanin.

Daga cikin dan babbar yayar Shugaban kasa Fatuhu Muhammad, wanda ya sha kashi hannun Aminu Jamo, rahoton Vanguard.

Dan'uwan Buhari, da wasu yan majalisar Katsina 6 da suka sha kashi a zaben fidda gwani
Dan'uwan Buhari, da wasu yan majalisar Katsina 6 da suka sha kashi a zaben fidda gwani
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit ta kawo muku jadawalin yan takaran da suka sha kasa tare da sunayen wadanda suka kayar da su.

MazabaYan majalisar da suka sha kashi da kuri'un da suka samuWadanda suka samu nasara da kuri'un da suka samu
Daura/Mai’Adua/ Sandamu Fatuhu Muhammad (30)Aminu Jamo (117)
Faskari/Sabuwa/ Dandume Murtala Isa (5)Dalhatu Tafoki. (96)
Katsina central Salisu Isansi (7)Sani Danlami (51)
Batagarawa/Rimi/Charanchi Hamza Dalhatu (56) Usman Banye (77)
Safana/Danmusa/ Batsari Ahmed Dayyabu Abdulkadir Zakka
Kurfi/Dustin Ma Armayau Kado (8)Aminu Balele (97)
Mani/Bindawa Ashiru Mani (54)Ahmed Yusuf (56)

Kara karanta wannan

APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 7 za su rasa kujerunsu a 2023

Dukka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

A shiyyar kudancin Katsina, Hon. Muntari Dan Dutse ya yi galaba a kan Sanata Bello Mandiya. Hon. Dan Dutse ya doke Sanata mai ci da ratar kuri’u fiye da 280.

‘Dan majalisar Zango/Baure, Nasir Sani Zangon Daura shi ne zai yi wa APC takarar Sanata a yankin Daura bayan ya doke tsohon kwamishina, Mustapha Kanti.

A yanki Daura kuwa, Sanata Ahmed Babba Kaita zai sake neman takarar majalisar dattawa na shiyyar Arewacin Katsina, wannan karo ‘Dan majalisar zai tsaya ne a PDP.

Jam’iyyar PDP ta tsaida Babba Kaita ya yi mata takarar Sanata a 2023, bayan ya fice daga APC. Shi kadai ne Sanata mai-ci da zai nemi tazarce a shekara mai zuwa.

A yankin Funtua, Kanal Abdulaziz Musa ‘Yaradua (mai ritaya) ya yi nasara a wajen lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Yadda duka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

Abdulaziz Musa ‘Yaradua ya doke Sanata Abdullahi Barkiya wajen samun tikitin majalisar dattawa, shi ne wanda zai yi wa APC takara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel