Ra'ayi: Bidiyon mutumin da ya kashe N6.2m saboda ya siffanta da kare ya ba da mamaki
- Wani mutum dan kasar Japan mai suna Toko ya kashe makudan kudade har Naira miliyan 6.2, kwatankwacin dalar Amurka 15,000 domin kawai ya siffantu da surar kare
- Toko, masoyin kare ya zuba wa wani kamfanin kasar Japan kudade ne don nemo masa wata suturar da za ta ba shi damar yin kama da karen turawa
- Jama'a a kafofin sada zumunta sun mayar da martani sosai game da bakon lamarin yayin da wasu ke tambayar dalilin da ya sa mutumin ya dauki wannan mataki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Japan - Toko, wani masoyin kare kare ne dan kasar Japan, wanda ya nemi wani kamfani wanda ya kera masa suturar da ta canza masa kama ya koma tamkar kare.
Wani faifan bidiyo ya nuna mutumin da ke sanye da kayan masu siffar kare kuma hakan ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta tare dubban tambayoyi, inda jama'a ke son sanin abin da yasa ya dauki wannan mataki.
Burinsa ne na tsawon rayuwarsa
An ce wani kamfani mai suna Zepet ne ya samar Toko da wannan samfurin sutura mai ban mamaki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan da hotunansa syuka shiga yanar gizo, sai suka yadu cikin sauri kuma suka haifar da martani daga bakunan jama'a/
Duk da haka, mutumin ya dage cewa burinsa na tsawon rayuwarsa ne ya zama mai kama da siffar kare.
First Post ne ya nakalto Toko wanda ya shaidawa wata kafar labarai ta gida, news.mynavi cewa:
“Wacce ma fi a cikin dabbobi su ne masu rub da ciki, musamman kyawawan dabbobi. A cikin su, na yi tunanin cewa babban dabbar da ke kusa da ni zai ta fi kyau, la'akari da cewa zai zama samfurin gaske, don haka na zabi amfani da kare."
Daga baya kafar yada bidiyo na @Ladbible ya wallafa bidiyon mutumin da ke cikin samfurin karen a shafin Instagram.
Kalli bidiyon:
Martanin 'yan Instagram
@bilyan_bozhidarov_21 yayi sharhi:
"Ina jin kamar ina can cikin zurfin yanar gizo."
@davetheyogi ya ce:
"Ya dai fi zuwa gyaran asibiti."
@jedhorspole yayi sharhi:
"Ka yi tunanin wannan a ce danka ne, wacce irin tambaya za ka yi na yanda ka reneshi."
@mattaqua ya amsa:
"A zahiri ya yi kyau, ina jiran mutumin ya fito."
@maira_saleemr said:
"Ya Allah! Gaskiya me duniya ke koma ne?"
Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya
A wani labarin, farashin kudin kwalliyar zamani da ake yiwa amare da kawayensu na farawa daga N5000 zuwa N100,000, dangane da mai kwalliyar da irin kayan da akayi amfani.
Amma wasu masu sana'ar kwalliyan kan shiga uku idan suka tafka kuskure musamman kan amare.
Da alamun irin haka ya faru a wani bidiyon da ya bazu a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng