Lafiyarsa lau: Jami'an gidan yari sun magantu kan yanayin da Abba Kyari ke ciki

Lafiyarsa lau: Jami'an gidan yari sun magantu kan yanayin da Abba Kyari ke ciki

  • Jami'an magarkama sun bayyana gaskiyar abin da ya faru da Abba Kyari a gidan yari, sun ce lafiyarsa kalau
  • Jami'an sun ce, lafiyar Abba Kyari kalau, kuma babu wanda ke bibiyar rasuwarsa da sunan za a cutar dashi
  • Hukumar ta ce ba shi ne farau ba a zaman gidan yarin Kuje, don haka babu abin da zai same shi saboda zaman cikinsa

Abuja - Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya (NCoS) ta yi watsi da rahotannin da ke cewa rayuwar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, na cikin hadari a gidan yari da ke Kuje, Abuja.

Ana tuhumar Kyari da laifukan da suka shafi safarar muggan kwayoyi kuma ana tsare da shi a Cibiyar Kula da Gyaran Hali ta Kuje, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu fursunoni da suka fusata sun kusa kashe Kyari, inda suka zarge shi da karbar cin hanci a wajensu a lokacin da yake aiki, yayin da yake ake ci gaba da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Magarkama Kuje ta yi bayani kan yanayin da Abba Kyari ke ciki
Lafiyarsa lau: Jami'an gidan yari sun magantu kan yanayin da Abba Kyari ke ciki | Hoto: dailytrust.com

Sai dai, Babban Kwanturolan gidan gyaran hali, Haliru Nababa, ya ce rahotannin barazana ga rayuwar Kyari "labari ne na karya".

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NSCoS, Francis Enobore ya sanya wa hannu a madadin CG din, hukumar ta ce:

“Labarin karya ne, shirme kuma yada barna.
“Dan kowa ya sani, Abba Kyari yana daya daga cikin fursunoni sama da 800 da ke wurin da ake tsare da shi kuma wasu fitattun mutane da suka hada da tsofaffin gwamnoni, Ministoci, Sanatoci da sauran fitattun mutane sun zauna a gidan yarin ba tare da wata barazana ba a rayuwarsu."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

Biyo bayan haka ne hukumar ta ce sam lafiyar Abba Kyari kalau, kuma babu wanda ke kokarin yi masa illa, kamar yadda PRNigeria ta ruwaito.

A cewar sanarwar:

“Abba Kyari yana cikin koshin lafiya kuma yana gudanar da al’amuransa na yau da kullun kamar kowane fursuna, ba tare da wata matsala ba."

Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

A wani labarin, an sake kawo dakataccen dan sanda Abba Kyari tare da wasu mutane shida kotu domin amsa laifukan safarar miyagun kwayoyi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ke zarginsu dashi.

Hukumar ta NDLEA ta shigar da laifuka takwas da suka hada da safarar miyagun kwayoyi kan Abba Kyari, wanda kuma ke ci gaba da fuskantar shari'a a Amurka saboda alakarsa da dan damfarar yanar gizo, Ramon ‘Hushpuppi’ Abbas.

Wadanda aka gurfanar tare da Kyari sun hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba, Insfekta John Nuhu, Chibuinna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

Kara karanta wannan

Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani

Asali: Legit.ng

Online view pixel