Rudadde ne: Dirama bayan da fasto ya ce zunubi ne miji ya yiwa matarsa ciki

Rudadde ne: Dirama bayan da fasto ya ce zunubi ne miji ya yiwa matarsa ciki

  • Wani mai bishara a wurin shakatawa kwanan nan ya yi wa’azi da yawa sama da haka sa’ad da ya bayyana cewa yin ciki zunubi ne.
  • A cewar malamin, mutum zai iya yin aure amma ba lallai ba ne mace ta kasance cikin ciki tunda Allah bai yarda ba.
  • Waɗanda yake yi wa wa’azi a cikin bas ɗin sun yi dariya sosai yayin da wasu suka yi ƙoƙari su yi masa magana, amma ya jajirce wajen wa’azin bishara

Wani mai wa’azi a Najeriya ya bullo da wani sabon salo a batun aure da haihuwa wanda jama'a da yawa suke dab da nuna kin amincewarsu.

Wani mai wa’azin da ya samu wuri a cikin wata mota ya bayyana ba tare da tauna kalamansa ba cewa miji ya dirkawa matarsa ciki zunubi ne.

Kara karanta wannan

Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim a Najeriya ta cire kunya

Wa'azin fasto ya jawo cece-kuce
Rudadden fasto: Martani bayan da fasto ya ce duk mijin da ya dirkawa matarsa ciki ya yi zunubi | Hoto: @instablog9ja and athima tongloom/Getty Images
Asali: UGC

An halatta aure amma ba a halatta yin ciki ba

Da'awarsa dai ta haifar da cece-kuce tun a cikin motar, inda wasu suka yanko masa ayoyin littafi mai tsarki na injila cewa, batun nasa ba akan daidai yake ba, inda suka ce ai ubangiji ya umarci 'yan adam su hayayyafa a doron kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma mai wa’azin da ba a ambaci sunansa ba ya dage kuma ya ki barin bahaguwar fassararsa na injila. @instablog9ja ne ya yada bidiyon abin da ya faru.

Yace:

"Shin dole ne? Shin duk wacce kuka yiwa ciki ne ke daukar ciki? Akwai wadanda kuke kwanciya da su ba za su dauki ciki ba. Don haka ciki zunubi ne, ku roki Allah ya gafarta maku."

Martanin 'yan Instagram

@sossiofficial ya ce:

"Haihuwa ba lallai ba ne...uban mutum ya sha barasar Regal."

Kara karanta wannan

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

@officialbobbyfredrick__ yayi sharhi da cewa:

"Don Allah ku bashi abinci, yunwa ke damunsa."

@adebrownie ya ce:

"Gaye wai kai wa ya kawo ka?"

@ladyque_1 ya ce:

"Yunwa ce ke damun wannan."

@callme_ekpo yayi sharhi da cewa:

"Yawancin wadannan masu wa'azin bas din na rantse idan sun ga abinci yanzun nan na tabbata za su daina."

@mz_ada023 yayi sharhi da cewa:

"Don Allah wani ya samo igiya a daure shi kada ya ciji wani."

Za mu sha farfesu: 'Yan Najeriya sun bar jama'a cikin mamaki bayan kamo kifin N500k a teku

A wani labarin, wani injiniyan ruwa mai suna Pakama da wasu abokan aikinsa biyu sun yi amfani da shafin Twitter don nuna babban kifin da suka kama a tekun da ke unguwar anchorage na jihar Legas.

Pakama ya yada hotunansa da abokan aikin nasa suna tare da babban kifin ya kuma rubuta: "Mun kama kifin yin farfesu."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya

Pakama mai shekaru 32 ya shaidawa wakilin Legit.ng, Victor Duru cewa sun kama kifin ne a ranar Talata, 25 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.