Kisan Fatima da 'yayanta: Muna binciken bidiyon don sanin sihhancinsa, Buhari

Kisan Fatima da 'yayanta: Muna binciken bidiyon don sanin sihhancinsa, Buhari

  • Daga karshe, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan bidiyon kisan wata 'yar Arewa da 'yayanta a Anambra
  • Shugaba Buhari ya ce ana kan gudanar da bincke kan bidiyon don sanin gaskiyar lamarin
  • Shugaban kasan ya yi kira ga yan Najeriya kada su yi wani abu da zai tada tarzoma a cikin jama'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Fadar shugaban kasa ta gargadi yan Najeriya kan yunkurin mayar da martani bisa bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta na kisan wata 'yar Arewa mai juna biyu tare da 'yayanta hudu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya fitar ranar Laraba yace Shugaba Buhari ya yi kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukunci kan bidiyon.

Buhari
Kisan Fatima da 'yayanta: Muna binciken bidiyon don sanin sihhancinsa, Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

Ya ce masana na gudanar da bincike kan bidiyon don sanin ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane.

A cewar jawabin:

"Fadar shugaban kasa na gargadi kan yunkurin tada tarzoma, lalata dukiya ko mayar da martani kan bidiyon da ake zargin yan kungiyar Eastern Security Network (ESN) da kashe yan ci rani."
"Yayinda masana ke gudanar da bincike kan gaskiyar bidiyon, muna kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin da ka iya tada tarzoma."

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kashe-kashen mutane da akeyi a yankin kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya.

CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyyar jihar Kaduna (CAN) ta yi Alla-wadai da kisar wata mata yar Arewa mai juna biyu tare da 'yayanta hudu a jihar Anambra, Kudu maso gabas.

Shugaban CAN na Kaduna, Joseph Hayab, ya ce ran kungiyar ya baci bisa wannan abu da ya faru.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

A jawabin da ya fitar yace Rayuwar dan Adam a kasar nan tayi arha saboda kowani sashe na da yan ta'adda

"CAN na yi kisan Fatima, jaririn dake cikinta da yayanta hudu da yan ta'adda sukayi a Anambra matsayin abu mara kyau ga zaman lafiya da hadin kan Najeriya."
"CAN na kira ga Gwamnatin tarayya ta nemo makasan Fatima da dukkan wadanda aka yiwa kisan gilla a Najeriya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel