Lamidon Adamawa ya bukaci Musulmai da su ji tsoron Allah
- Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, ya kalubalanci Musulmai da su ji tsoron Allah a koda yaushe
- Basaraken wanda ya bayyana hakan a yayin gasar Musabakar Al-Kur'ani ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmin da su kasance masu tuna mutuwa
- Har ila yau, ya bukaci iyaye da su baiwa yaransu musamman mata cikakken ilimin da ya dace a rayuwarsu
Adamawa - Mai martaba Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ji tsoron Allah tare da tuna mutuwa.
Basaraken ya bayyana hakan ne a yayin taron musabakar Kur’ani na kasa karo na 11 wanda aka yi a kwalejin ilimi na tarayya da ke garin Yola, Daily Trust ta rahoto.
Lamidon ya samu wakilcin Hakimi kuma Cika Soro Adamawa, Alhaji Muhammad Ahmad Mustapha.
Lamidon Adamawan ya kuma bukaci iyaye da su ilimantar da yaransu, musamman ma ‘ya’ya mata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban majalisar musulunci ta kasa, Alhaji Gambo Jika, yace an shirya taron ne domin sanya dabi’ar haddace kur’ani a tattare da dalibai mata daga makarantun sakandare a Najeriya.
Ya ce fiye da jihohi 20 tare da mutane 75 ne suka shiga gasar Al’Kur’ani na wannan shekarar wanda za a kammala a ranar Asabar.
Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba
A wani labarin, gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ba yan arewa ake nufin kashewa ba a jihar.
Soludo ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga kisan wata mata mai ciki da yaranta da wasu da ake zaton yan awaren IPOB ne suka yi, Daily Trust ta rahoto.
A cikin wata sanarwa daga Mista Christian Aburime, babban sakataren labaransam Soludo ya ce yan asalin Anambra, yan arewa da mutane daga sauran yankunan kasar suna zama tare da yin kasuwanci da juna cikin lumana, rahoton Daily Post.
Asali: Legit.ng