Malamin makaranta ya yi wa Dalibansa duka a aji, a karshe wani yaro ya mutu
- Wani dalibi da ke aji biyu a karamar sakandare ya mutu a sanadiyyar dukar da malaminsu ya yi masu
- Wannan abin ya faru ne a wata makaranta mai suna Simple Faith Schools garin Agbara, jihar Legas
- Karamin yaron mai shekara 12 ya cika ne a asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Legas da ke Surulere
Punch ta rahoto cewa Emmanuel Amidu da ke karatu a makarantar sakadaren Simple Faith Schools, ya mutu bayan malaminsa ya yi masa duka.
Mahaifin marigayin, Akinola Amidu ya shaidawa ‘yan jarida cewa malamin yaron na sa mai shekara 12, shi ya yi masa dukan da sai da aka je asibiti.
Akinola Amidu ya ce malamin da ke koyar da lissafi ya zane Emmanuel Amidu ne a wata ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022 lokacin da ya shigo aji.
Jim kadan bayan abin da ya faru, sai yaron ya fara amai, daga nan aka sheka da shi asibiti. ‘Yaruwar yaron ta shaidawa manema labarai wannan.
Rahoton ya ce a karshe wannan yaro mai shekara 12 da haihuwa ya cika ne a asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Legas da ke garin Surulere, a jihar Legas.
Mahaifin ya ce hukumar makarantar da ke Agbara ta na kokarin boye lamarin domin a rufawa wannan malamin na lissafi mai suna Mista Steven asiri.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Steven ya zane yaron ne saboda ba su kammala aikin gidan da aka ba su ba. Tun da aka bugi marigayin, ya fara rashin lafiyar da ake zargin ta yi ajalinsa.
Yadda abin ya faru - Mahaifinsa
A cewar Amidu a ranar da abin ya faru, ya ba yaron da ya rasu kudi domin ya saye littafi, daga baya sai aka kira shi daga makaranta cewa yaron yana amai.
“Alhali yaron nan ya bar gida lafiya ba tare da wani rashin lafiya ba. Dole na je makarantar, daga nan mu ka dauke shi zuwa wani asibiti.”
“Daga baya sai na fahimci ciwon ya fara ne bayan malamin ajinsu, Mista Steven ya zane duka ‘yan ajinsu saboda sun gaza yin aikin gida.”
“A LUTH yarona ya cika. Sai hukumar makarantar suka ruga ofishin ‘yan sanda na Morogbo a Agbara, su ka ce ya mutu ne wajen amai.”
Mu na neman hakkinmu
Akinola mai shekara 45 ya ce haka nan yaro ba zai fara amai ba sai da sababi, don haka ya bukaci jami’an tsaro su hukunta wannan malami da ke ba kariya.
Shugaban makarantar, Adetayo Akanji, ya ce malamin ya zane ‘yan aji biyu gaba daya, amma ba da niyyar cutarwa ba, daga nan ne Emmanuel ya kwanta.
Asali: Legit.ng