Yadda Rochas Okorocha ya kwanta a kasa yana rokon a taimaka masa yayin da EFCC ta kama shi

Yadda Rochas Okorocha ya kwanta a kasa yana rokon a taimaka masa yayin da EFCC ta kama shi

  • Dakaraun hukumar yaƙi da cin hanci EFCC sun kama tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha, bayan shafe awanni a gidansa
  • Wasu bayanai sun nuna cewa Sanatan ya kwanta a ƙasa yana rokon Allah ya kawo masa ɗauki shi da iyalansa kafin tasa keyarsa
  • Da yake jawabi ga manema labarai, Okorocha, ya nuna mamakinsa kan dalilin EFCC na yi masa haka

Abuja - Sanata Rochas Okorocha ya kwanta a ƙasan Siminti yana rokon a taimaka masa yayin da jami'an tsaro suka kewaye gidansa a Abuja ranar Talata.

Daily Trust ta rahoto yadda jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) suka dira gidan tsohon gwamnan da nufin kama shi.

Bayan ɗauƙar tsawon lokaci kusan awanni biyar a gidan, dakarun suka kutsa kai har cikin gidan Okorocha suka tasa keyarsa zuwa Ofishin su.

Kara karanta wannan

Okorocha ya fallasa hikimar aiko masa EFCC ana shirin zaben ‘Dan takarar Shugaban kasa

Rochas Okorocha.
Yadda Rochas Okorocha ya kwanta a kasa yana rokon a taimaka masa yayin da EFCC ta kama shi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Karar harbe-harben bindiga ya cigaba da tashi cikin iska yayin da jami'ai suka kutsa cikin ɗakin hutun Okorocha na alfarma inda shi da iyalansa suka kwanta a ƙasa don kauce wa Alburushi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani sakon murya an ji tsohon gwamnan na Imo na cewa:

"Dan Allah a taimake ni, ku cece ni. Ubangiji na ka zo ka taimake ni, Ya Allah ka zo ka ceci rayuwata."

Bayan haka wani Bidiyo da ya bayyana ya nuna Sanatan na cewa watakila wannan ne karo na karshe da za'a ganshi da daddare.

"EFCC ta zo nan gidana da wasu yan bindiga, sun lalata duk rigunan kariya na, wannan ne gani na na karshe. Sun zo da nufin harbi," Okorocha ya faɗa a takaice kafin a zagaye shi.

Bayan kama Okorocha, bayanai sun nuna cewa an samu wata yar hatsaniya tsakanin wasu mutane da ake zargin hadimansa ne da kuma jami'an EFCC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Duk da babu wanda ya san abin da ya jawo hayaniyar amma Toyota Hiace fara wacce aka tilasta wa Sanatan shiga ciki ta ɗauki mintuna uku kafin ta shiga jerin gwanon motocin jami'an tsaron da suka zagaye gidan.

Meyasa EFCC ta kama Sanatan na APC?

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce sun yi haka ne biyo bayan rashin amsa gayyatar da suka tura wa tsohon gwamnan lokuta da dama.

Hakanan kuma ya ƙara da cewa Okorocha ya tsallake belin da hukumar EFCC ta ba shi tun da farko.

A.wani labarin kuma Wani gwamna ya ziyarci Sakatariyar APC ta ƙasa, ya sa labule da shugaban jam'iyya

Gwamnan jahar Ogun, Dapo Abiodun, ya ziyarci babbar Sakatariyar APC ta ƙasa ranar Talata, ya gana da shugaban jam'iyya.

Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya tarbi gwamnan zuwa ganawar sirri ta tsawon awa ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262