Gwamna Abiodun ya gana da shugaban APC na ƙasa a Sakatariyar jam'iyya Abuja

Gwamna Abiodun ya gana da shugaban APC na ƙasa a Sakatariyar jam'iyya Abuja

  • Gwamnan jahar Ogun, Dapo Abiodun, ya ziyarci babbar Sakatariyar APC ta ƙasa ranar Talata, ya gana da shugaban jam'iyya
  • Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya tarbi gwamnan zuwa ganawar sirri ta tsawon awa ɗaya
  • Sai dai gwamnan bai faɗa wa yan jarida komai ba game da abin da suka tattauna ba, yana fitowa ya shiga mota ya bar wurin

Abuja - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ziyarci babbar Sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Talata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya samu kyakkyawar tarba da maraba daga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ba da ɓata lokaci ba suka shiga ganawar sirri.

Jam'iyyar APC ta ƙasa.
Gwamna Abiodun ya gana da shugaban APC na ƙasa a Sakatariyar jam'iyya Abuja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Duk wani yunƙurin jin ta bakin gwamna Abiodun bayan fitowa daga taron wanda ya shafe awa ɗaya ya ci tura kasancewar ya yi watsi da yan jarida, ya shiga motarsa ya bar wurin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Aisha Buhari, Ministar mata da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC

Gwamnan nan dai ya shiga tsaka mai wuya ta wata badaƙala da ake zargin ya na da tarihin aikata babban laifi a ƙasar Amurka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma gwamnan ya samu saɓani da mambobin jam'iyyar APC reshen Ogun da kuma wakilai, wanda ta kai ga suka kai ƙorafinsa ga uwar jam'iyya ta ƙasa kan bukatar yin zaɓen kato bayan ƙato a Ogun.

NANS ta kai korafin Abiodun

Bayan haka kungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa (NANS) shiyyar D ta rubuta korafi kan gwamnan kuma ta aika wa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da kuma Sanata Adamu.

Ƙorafin ya samu sa hannun kakakin ƙungiyar NANS, Victor C. Ezenagu, da kuma shugaban majalisar NANS, Chuks Okafor.

A korafin, kungiyar ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ɗauki mataki kuma su hana gwamnan neman zarcewa a kan kujerarsa ta gwamna a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin jam'iyyar PDP guda uku sun sa labule da Obasanjo

A wani labarin na daban kuma Wani ɗan takara a PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta ƙasa a jihar Delta, Philip Okwuada, ya sume bayan jin yadda ta kaya a zaɓen fidda gwani.

Bayanai sun nuna cewa ɗan siyasan ya samu tabbacin samun nasara kafin zaɓen amma Deleget suka yaudare shi ya sha ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel