Yan bindiga sun buɗe wa motar ɗan takarar APC wuta a Borno, rayuka sun salwanta

Yan bindiga sun buɗe wa motar ɗan takarar APC wuta a Borno, rayuka sun salwanta

  • Wasu miyagun yan bindiga sun mamayi jerin gwanon ɗan takarar Sanata a APC, sun buɗe musu wuta da safiyar Lahadi a Borno
  • Rahoto ya nuna cewa yan sanda biyu sun rasa rayukan su yayin da wasu magoya baya da dama ke kwance a Asibiti sanadin harin
  • Wani makusancin ɗan takarar ya ce rayuwar uban gidan su na cikin hatsari bayan wannan harin, Allah ya sa baya cikin motarsa

Borno - Ɗan takarar sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Alhaji Idris Durkwa, wanda ke kan gaba wajen samun tikiti ya tsallake rijiya da baya yayin da yan bindiga suka farmaki tawagar motocinsa.

Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan sun yi wa jerin gwanon motocinsa kwantan ɓauna suka bude musu wuta a kan hanyar Maiduguri-Damaturu ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Bayan kokarin sulhu, Gwamna ya shata layin yaƙi da yan bindiga, ya ce zai hana su sakat

Aƙalla yan sanda biyu suka rasa rayukansu yayin da wasu masoyan ɗan siyasan da dama suka jikkata yayin harin yan ta'addan.

Alhaji Idris Durkwa.
Yan bindiga sun buɗe wa motar ɗan takarar APC wuta a Borno, rayuka sun salwanta Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun yi tsammanin ɗan takarar na cikin tawagar motocin waɗan da ke kan hanyar zuwa Maiguduri daga Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin wani abu ya samu ɗan siyasan?

Sai dai bisa rashin sa'a, Ɗan takarar Sanatan baya cikin motocin, rahoto ya nuna cewa yana can Maiduguri domin tarban wasu dandazom magoya bayansa.

Haka zalika a bayanan da aka tattara bayan harin, motar da ɗan siyasan, wato Durkwa ya saba hawa a kowane lokaci, maharan sun danna mata harsashi 12.

Da aka tuntuɓi ɗaya ɗaga cikin makusantansa, wanda ya nemi a boye bayanansa ya tabbatar da kai wa motocin hari.

Ya ce:

"Rayuwar ɗan takarar mu na Sanata, Alhaji Idris Durkwa, na cikin hatsari, maƙiyansa na yi wa rayuwarsa barazana kan matakin shiga neman tikitin kujerar Sanata mai wakiltar kudancin Borno."

Kara karanta wannan

Fusatattun mutanen gari sun lakaɗawa wani da dubunsa ta cika dukan tsiya har Lahira a Katsina

"Ranar Lahadi da karfe 10:00 na safe mahara suka farmaki jerin gwanon motocinsa ɗauke da ɗaruruwan magoya baya a hanyar Damaturu-Maiduguri. Yan sanda biyu sun mutu wasu da dama na kwance a Asibiti."
"Na yi takaicin yadda aka kaiwa motocin hari bayan hanyar ta samu zaman lafiya na tsawon lokaci kuma ina mamakin yadda sai a yanzun abun ya faru, bayan Sojoji sun ayana hanyar cikin masu zaman lafiya."

A wani labarin kuma Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim ta cire kunya

Jaruma a masana'antar shirya Fina-Finai Nollywood, Eucharia Anunobi, ta sanar da duniya halin da take ciki na bukatar mijin aure.

Yayin zantawa da kafar watsa labarai, Jarumar ta ce tana son mijin da zata aura ya gaggauta bayyana kuma ya zama cikakken namiji, kyakkyawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262